Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa

Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa

Atiku Abubakar ya sake yin magana biyo bayan kama surukinsa, Babalele Abdullahi da lauyansa cewa suna biyan bashin mara masa baya da suka yi ne.

Atiku ya fadi zaben Shugaban kasa inda Muhammadu Buhari yayi nasara koda dai dan takarar na jam’ iyyar Peoples Democratic Party ya ki amincewa da sakamakon zaben sannan ya sha alwashin zuwa kotu.

Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa
Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa
Asali: Facebook

Atiku a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar 4 ga watan Maris, yayi kira fa wadanda ke hukunta su da su tuna cewa gwamnati aba ce da ake sanya ran za ta wanzar da zaman lafiya ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.

KU KARANTA KUMA: Sanata Dariye na fama da matsalar gazawar koda a gidan yari

Ya rubuta cewa: “An tsare surukina da lauyana, daya tsawon makonni 3 sannan dayan kuma kwanan nan aka kama shi. Duk suna biyan bashin mara mun baya da suka yi ne. Ina bukatar wadanda suke hukuntasu dan su tuna cewa hakkin gwamnati shine ta wanzar da zaman lafiya da yin adalci ga kowa, ba wai wadanda suka mara masu baya ba kawai.”

A baya mun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Jama’til Nasaril Islam, Alhaji Sa’adu Abubakar III ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara a zaben 2019 daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu.

Sai dai Sarkin Musulmai yayi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya sha kayi a hannun Buhari, daya rungumi kaddara, ya saduda, kuma ya rungumi zaman lafiya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel