Masu neman Gwamna a Jihar Kano sun ziyarci Kwankwaso da Abba Yusuf

Masu neman Gwamna a Jihar Kano sun ziyarci Kwankwaso da Abba Yusuf

Mun samu labari cewa a cikin ‘yan kwanakin wasu ‘yan takaran jam’iyyun adawa a jihar Kano sun kai wa tsohon gwaman Rabiu Musa Kwankwaso ziyara yayin da ake shirin zaben gwamnonin jihohi.

Masu neman Gwamna a Jihar Kano sun ziyarci Kwankwaso da Abba Yusuf
Mai neman Gwamna Mohammed Abacha ya gana da Kwankwaso
Asali: Twitter

Kamar yadda labari ya zo mana, ‘dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APDA mai adawa, Alhaji Muhammad Sani Abacha, ya gana da Madugun Kwankwasiyya watau Sanata Rabiu Musa Kwankwaso,

Mohammed Abacha wanda yana cikin wanda su kayi takara da Rabiu Musa Kwankwaso a lokacin yana jam’iyyar CPC, yayin da Kwankwaso yake PDP a 2011, ya bayyana Kwankwaso a matsayin babban Yayan sa a siyasa.

KU KARANTA: Har abada Atiku ba zai kira Buhari ya taya sa murna ba - PDP

Bayan Muhammad Abacha, ‘dan takarar jam’iyyar NRM watau Alhaji Muhammad Shehu ya zauna da jigon na PDP, Rabiu Kwankwaso da kuma ‘dan takarar gwamna a PDP watau Injiniya Abba K. Yusuf a gidan sa.

Wani Hadimin tsohon gwamnan na Kano, ya kuma bayyana mana cewa Alhaji Ahmed Sawaba na jam’iyyar GDPN ya zauna da Rabiu Kwankwaso domin ganin yadda za a tika Abdullahi Ganduje da kasa a zabe bana.

Labari ya zo mana har wa yau cewa, Hajiya Maimuna Muhammadu, ta gana da Jagoran na Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso a gidan sa. Muhammadu tana takara ne a karkashin jam’iyyar UPP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel