Da duminsa: Kungiyar JUSUN ta garkame babban alkalin jihar Nasarawa a ofishinsa

Da duminsa: Kungiyar JUSUN ta garkame babban alkalin jihar Nasarawa a ofishinsa

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa mambobin kungiyar ma'aikatan sharia karkashin inuwar kungiyar JUSUN reshen jihar Nasarawa, sun garkame babban alkali na jihar Nasarawa, mai shari'a Suleiman Umar Dikko a cikin ofishinsa.

JUSUN na ikirarin cewa babban alkalin jihar na rage wani kaso daga cikin albashin kowanne ma'aikaci a shekara.

Idan za a iya tunawa, kungiyar JUSUN ta shiga yajin aiki tun a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2018.

KARANTA WANNAN: A karshe: Mun gano wadanda ke haddasa rikicin jihar Benue - Rundunar soji

A halin yanzu dai an kara yawan jami'an tsaro a kotunan da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel