Zaben gwamna: Kanwar Saraki ta mara wa APC baya

Zaben gwamna: Kanwar Saraki ta mara wa APC baya

- Yar'uwar shugaban majalisar dattawa, Sanata Gbemisola Saraki tace za ta tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress don ganin ya lashe zaben gwamna da aka shirya gudanarwa a ranar 9 ga watan Maris

- Saraki ta kara da cewa dan takarar APC, AbdulRahman AbdulRasaq zai kora jam’ iyyar PDP mai mulki a jihar gida

- Tace ya zama dole jihar Kwara ma ta bi sahun Next Level a ranar Asabar mai zuwa

Sanata Gbemisola Saraki a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris tace za ta tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress don ganin ya lashe zaben gwamna da aka shirya gudanarwa a ranar 9 ga watan Maris.

Yar’uwar Shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki na jam’iyyar the Peoples Democratic Party, ta kara da cewa dan takarar APC, AbdulRahman AbdulRasaq zai kora jam’ iyyar PDP mai mulki a jihar gida.

Zaben gwamna: Kanwar Saraki ta mara wa APC baya
Zaben gwamna: Kanwar Saraki ta mara wa APC baya
Asali: UGC

Tsohuwar yar majalisar wacce ta bayyana hakan a wani jawabi ta yi ikirarin cewa jihar za ta bi sahun jirgin “Next Level” a ranar Asabar mai zuwa.

Tace: "Ba za mu hana nasara jagorantar dukkanin jihohi zuwa mataki na gaba ba domin ci gabanmu.

KU KARANTA KUMA: Mutanen Kano sun dade suna bani goyon baya tun a 2003 - Buhari

“Don haka domin amfanin kowa, ya zama dole mu jajirce, a ranar Asabar, 9 ga watan Maris ne za a gudanar da zaben.

“A jiha ta Kwara, dukkaninmu za mu tabbatar da ganin cewa AbdulRahman AbdulRasaq na jam’ iyyarmu ta APC ya zama gwamnan jihar Kwara na gaba, Insha Allah.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel