Nasarar Atiku a kotu: Da kamar wuya - Babban lauyan Femi Falana

Nasarar Atiku a kotu: Da kamar wuya - Babban lauyan Femi Falana

Shahrarren dan yakin kare hakkin dan Adam, Barista Femi Falana, ya bayyana cewa da kamar wuya dan takaran jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kayar da shugaba Muhammadu Buhari idan ya tafi kotu.

Kana ya bayyana cewa da Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasara a ranar Asabar da ya gabata, da abin ya bashi mamaki saboda yayinda shugaba Buhari ke alfahari da gaskiya da amana, Atiku na kokarin kare nasa mutuncin ne.

Yace: "Da abin ya bani mamaki da Atiku ya lashe zaben. Saboda nasararsa na da illa ga Najeriya. Sai ya kare dukkan maganganun batancin da tsohon shugaba Obasanjo yayi akansa."

"A yanzu haka kasar Amurka na gudanar da bincike akansa. Bai taba musanta cewa yanada niyya azurta abokansa ba. Atiku ya yi niyyar sayarwa abokansa kamfain NNPC."

Da aka tambayesa shin Atiku zai iya samun nasara a kotu, Falana yace: "Da kamar wuya."

KU KARANTA: Buhari zai rage ratar da ke tsakanin Mai kudi da Talaka – Inji Matar sa

A bangare guda, mun kawo muku cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Jama’til Nasaril Islam, Alhaji Sa’adu Abubakar III ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara a zaben 2019 daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu.

Sai dai Sarkin Musulmai yayi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya sha kayi a hannun Buhari, daya rungumi kaddara, ya saduda, kuma ya rungumi zaman lafiya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel