Sanata Dariye na fama da matsalar gazawar koda a gidan yari

Sanata Dariye na fama da matsalar gazawar koda a gidan yari

An dauke tsohon gwamnan jihar Plateau kuma Sanatan Plateau ta tsakiya, Joshua Dariye daga gidan yari zuwa wani asibiti bayan ya kamu da cutar gazawar koda.

An tattaro cewa an kwashi Dariye wanda aka yankewa shekaru 10 a gidan yari saboda satar kudin kasa zuwa asibitin koyarwa na Abuja, Gwagwalada tun a watan Disambar da ya gabata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wata majiya kusa da tsohon gwamnan ta fada ma yan jarida cewa baya cikin kyakyawar yanayi.

Dan majalisan, wanda ya kasance a kurkukun Kuje dake Abuja ya kasance a asibiti tun watar Disamba da ya gabata.

Sanata Dariye na fama da matsalar gazawar koda a gidan yari
Sanata Dariye na fama da matsalar gazawar koda a gidan yari
Asali: Depositphotos

A cewar majiyin gwamnati wanda ya nemi a boye sunansa yace Dariye na matukar bukatan addu’a sosai.

Majiyin yace: ”na je ganin shi. Daga binciken likitoci, yana fuskantar kalubale a kiwon lafiyarsa, yana matukar fama da matsalar koda.

KU KARANTA KUMA: Mutanen Kano sun dade suna bani goyon baya tun a 2003 - Buhari

Kakakin hukumar Firson na Najeriya (NPS), reshen Babban Birnin Tarayya Chukwuedo Humphrey, ya tabbatar da cewa Dariye na a asibiti, amman ya ki bayyana yanayin ciwon.

Ya ce tun daga watan Oktoba na shekaran da ta gabata ne hukumar ke kula da rashin lafiyarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel