Mutane na barin Garin Abonnema a dalilin kisan wasu Soji 2 kwanan nan

Mutane na barin Garin Abonnema a dalilin kisan wasu Soji 2 kwanan nan

Mutane da dama su na ficewa daga cikin Kauyen Abonnema da ke cikin karamar hukumar Akuku Toru a jihar Ribas bayan an kashe wasu sojojin Najeriya har 2 a daren Ranar Asabar dinnan da ta gabata.

Mutane na barin Garin Abonnema a dalilin kisan wasu Soji 2 kwanan nan
Ana tsoron Sojoji su dauki fansa bayan an hallaka wasu Jami’an tsaro
Asali: Facebook

Mutanen da ke cikin wannan kauye na Abonnema, sun ji tsoron cewa sojoji na iya kawo masu harin mai uwa da wabe, a dalilin kisan da aka yi wa Abokan aikin su. Jami’an ‘yan sandan yankin sun tabbatar mana da wannan.

Omoni Nnamdi, wanda shi ne kakakin ‘yan sanda na jihar Ribas, ya bayyanawa manema labarai cewa mutane da dama su na tserewa daga cikin karkarar Abonnema, tun da aka kashe wasu Dakarun sojoji a 'yan kwanakin nan.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai ba Matasa mukamai inji Aisha Buhari

Wasu ‘yan bindiga ne dai masu dauke da kayan sojoji su ka kai wa rundunar sojojin Najeriya hari a karshen makon da ya wuce. ‘Yan bindigan sun kashe sojoji har 2, yayin da kuma su ka raunata wasu jami’an tsaro da dama.

Wannan mummunan abu ya faru ne a daidai kan iyakar titin Obonoma zuwa Abonnema inda jami’an tsaro ke tsayawa. Hakan na zuwa ne dai bayan an kashe wasu mutum 6 a ranar da aka yi zaben shugaban kasa a yankin.

Har yanzu dai jami’an sojojin Najeriya ba su ce uffan game da wannan kisa da aka yi masu ba. Jama’a dai sun sha jinin jikin su, sun fice daga garin domin gudun sojoji, su dawo daukar fansa nan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel