Kaico! Yadda miyagu suka kashe wani mutumi yana Sallah a jahar Kano

Kaico! Yadda miyagu suka kashe wani mutumi yana Sallah a jahar Kano

Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da kama wasu miyagun matasa guda biyu marasa Imani da take zargi da kashe wani mutumi mai suna Adamu Bala yayin da yake gudanar da Sallar, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar Kano.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, 5 sun mutu, 10 sun jikkata

Kaakaki DSP Abdullahi Haruna ya bayyana sunayen wadannan miyagu kamar haka; Kamalu Musa da Babangida, dukkaninsu mazauna unguwar Shekar Madaki dake cikin garin Kano.

A jawabinsa, kaakakin ya bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar 27 ga watan Feburairu, inda Babangida da Kamalu Musa suka lallaba suka kashe Adamu Bala a lokacin da yake salla a wani gidan buga bulo dake Bubugaje.

Daga karshe kaakakin yace a yanzu haka sun kaddamar da bincike don gano dalilin da yasa miyagun suka kashe mamacin, sa’annan ya bada tabbacin zasu tabbatar da an hukunta matasan yadda ya kamata.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Kano ta kama wani dan daba mai suna Salisu Muhammad da laifin caka ma wani mutumi Mujittafah Musa wuka, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Maris da misalin karfe 11:21 na dare yayin da musun kwallo ta hadasu, inda daga nan Salisu ya dauki wuka ya daba ma Mujittafa wuka a kirjinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel