Zaben 2019: Sultan yayi kira da babban murya ga Atiku Abubakar

Zaben 2019: Sultan yayi kira da babban murya ga Atiku Abubakar

Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Jama’til Nasaril Islam, Alhaji Sa’adu Abubakar III ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara a zaben 2019 daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu.

Sai dai Sarkin Musulmai yayi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya sha kayi a hannun Buhari, daya rungumi kaddara, ya saduda, kuma ya rungumi zaman lafiya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, 5 sun mutu, 10 sun jikkata

Zaben 2019: Sultan yayi kira da babban murya ga Atiku Abubakar
Sultan da Atiku
Asali: UGC

Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kungiyar JNI ta fitar a ranar Lahadi a babban ofishinta dake garin Kaduna ta bakin babban sakataren hukumar, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, inda yace JNI na godiya ga Allah daya tabbatar da zaman lafiya a zaben daya gabata.

“Muna godiya ga ubangiji Allah mai rahama mai jin kai sakamakon gudanar da zaben shugaban kasa dana yan majalisun da aka yi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, har aka sanar da wanda ya samu nasara.

"Don haka Jama’atu Nasril Islam a karkashin jagorancin Sarki Muhammadu Sa’ad Abubakar na taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murna da sauran wadanda suka samu nasara, da kuma yan Najeriya da suka gudanar da kansu yadda ya kamata.

“Sai dai muna kira ga duk masu ruwa da tsaki a siyasan Najeriya dasu ji tsoron Allah su mayar da wukakensu, kuma su sani cewa a duk takara akwai wanda zai samu nasara da kuma wanda zai samun rashin nasara.

“Amma a wannan takarar, dukkanin yan takarar sun samu nasara, musamman saboda yan Najeriya sun fara fahimtar yadda ake gudanar da siyasa a mulkin dimukradiyya.” Inji sanarwar kungiyar JNI.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel