Sambo Dasuki yana nan lafiya kalau bai mutu ba – Inji Hukumar DSS

Sambo Dasuki yana nan lafiya kalau bai mutu ba – Inji Hukumar DSS

Labari ya zo mana daga NTA game da halin da tsohon mai bada shawara kan harkar tsaro a Najeriya watau Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) yake ciki, bayan ana ta rade-radin cewa ya mutu kwanan nan.

Sambo Dasuki yana nan lafiya kalau bai mutu ba – Inji Hukumar DSS
Gwamnatin shugaba Buhari ta cafke Sambo Dasuki tun 2015
Asali: UGC

Hukumar jami’an tsaro masu fararen kaya a Najeriya na DSS, sun musanya cewa wani abu ya faru da Kanal Sambo Dasuki. DSS ta bakin kakakin ta, tace labarin da ake ta yadawa na cewa Sambo Dasuki ya rasu ba gaskiya bane.

Peter Afunanya, wanda shi ne mai magana da yawun bakin hukumar tsaron, ya fadawa gidan talabijin na NTA na kasa cewa Sambo Dasuki yana nan kalau. Afunanya yace tsohon NSA na kasar nan yana nan cikin koshin lafiya.

KU KARANTA: Masu kashi a jikin su ba za su ji kanshin gwamnati na ba - Buhari

Kwanan nan ne aka yi ta jita-jita a shafukan yanar gizo cewa S. Dasuki wanda ya taba rike matsayin mai ba shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara a kan harkar tsaron Najeriya, ya rasu yayin da yake tsare wajen hukuma.

Kakakin na DSS ya karyata wannan sannan yana mai tir da irin wadannan karyayyaki da mutane su ke ta yadawa. Yanzu dai gwamnatin Najeriya ta shafe fiye da shekaru 3 tana rike da Sambo Dasuki bisa zargin cin kudin tsaro.

Ana ci gaba da tsare Sambo Dasuki ne duk cewa an nemi a bada belin sa. Bayan kotun gida Najeriya, har kotun ECOWAS ta Afrika ta bada umarni a saki Dasuki, amma gwamnatin Buhari tayi ta daga kara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel