An sake kwatawa: Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, 5 sun mutu, 10 sun jikkata

An sake kwatawa: Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, 5 sun mutu, 10 sun jikkata

Rundunar Yansandan jahar Kaduna ta tabbatar da wani mummunan hari da wasu gungun yan bindiga da ba’a san daga inda suka fito ba suka kai kauyen Sabon Sara na cikin karamar hukumar Giwa ta jahar Kaduna, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Yakubu Sabo ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Lahadi, 3 ga watan Feburairu, inda yace maharan sun kashe mutane biyar, sun jikkata wasu mutum goma.

KU KARANTA: Bincike ya bayyana Ganduje zai sake lashe zaben gwamnan jahar Kano

Sai dai DSP Sabo yace wani guda daga cikin wadanda suka jikkata ya mutu a asibiti. Wannan shine ba’a rabu da bukar ba an samu abu, duba da cewa ba’a kammala shawon kan hare hare da ake kaiwa yankin karamar hukumar Birnin Gwari ba, sai ga shi ta bulla a Giwa.

Kaakakin ya cigaba da cewa an sallami mutane uku daga cikin wadanda suka jikkata, yayin da sauran mutane shidan suke cigaba da samun kulawa a asibiti, haka zalika yace suma mazauna kauyen basu yi kasa a gwiwa ba yayin da yan bindigan suka shigo.

“A yayin da yan bindigan suka fada kauyen, jama’a sun yi kokarin hada kansu, inda suka far ma yan bindigan har suka samu nasarar kashe dan bindiga daya, ko da tawagar Yansanda na musamman suka isa garin, tuni yan bindigan sun tsere.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Sabo ya tabbatar ma al’ummar dake zaune a yankin cewa rundunar Yansanda na iya kokarinta don ganin ta kama duk masu hannu cikin hare haren tare da hukuntasu kamar yadda doka ta tanadar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel