Bincike ya bayyana Ganduje zai sake lashe zaben gwamnan jahar Kano

Bincike ya bayyana Ganduje zai sake lashe zaben gwamnan jahar Kano

A yayin daya rage saura kwanaki hudu a gudanar da zaben gwamnonin Najeriya, wasu alkalumma da aka samu daga binciken masana sun nuna wasu gwamnonin Najeriya da ake ganin zasu kai bantensu a zabe, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito na gaba gaba a cikin wadannan gwamnoni shine gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jahar Ribasm Nyesoma Wike, da gwamnan jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal.

KU KARANTA: Atiku bai nemi wasu bukatu a wajen Shugaba Buhari ba – Inji PDP

Bincike ya bayyana Ganduje zai sake lashe zaben gwamnan jahar Kano
Wike, Tambuwal da Ganduje
Asali: UGC

Wata kungiya mai zaman kanta, ANAP Foundation ce ta gudanar da wannan bincike, kungiyar ta kwashe tsawon shekaru tana gudanar da bincike akan zabukan Najeriya, tun daga shekarar 2011, inda tace tana yin hakan ne don ta samar da shugabanci nagari.

Sai dai akalumman binciken sun nuna dan takarar gwamnan jahar Legas a inuwar jam’iyyar APC, Babajide Sanwo Olu bashi da wata garantin samun nasara saboda kaso 53 na cikin masu zabe a Legas da suka tattauna da kungiyar ANAP basu yanke shawarar zabensa ko akansin haka ba.

Game da jahar Kano kuwa, alkalumman sun nuna za’a kusan kankankan tsakanin Ganduje da dan takarar gwamnan jahar Kano najam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, amma dai Ganduje zai kai bantensa.

Daga cikin sakamakon da binciken ya bankado shine akwai wani kaso na jama’an Kano dake goyon bayan Ganduje da suka hada da mata da suka amfana da tallafi kashi 21, wadanda suka aminta dashi 17%, masu son ya zarce 17%, tallafa ma matasa 11% da kuma wadanda suka gamsu da aikinsa 9%.

Sai dai a daya hannun, su kuma masu son Abba sun hada da masu son ganin an canza gwamnati 20%, wadanda Abba ke burgesu 25%, zabin farko 20%, masu sonshi 9% da kuma wadanda suke ganin yana da hazaka 5%.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel