Atiku bai nemi wasu bukatu a wajen Shugaba Buhari ba – Inji PDP

Atiku bai nemi wasu bukatu a wajen Shugaba Buhari ba – Inji PDP

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya ta PDP ta fito tayi bayani game da jita-jitar da ake yi na cewa ‘dan takarar ta a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar yana da wasu bukatu wajen shugaba Buhari.

Atiku bai nemi wasu bukatu a wajen Shugaba Buhari ba – Inji PDP
PDP ta hakinkance a kan cewa Buhari bai ci zabe ba
Asali: Facebook

Jam’iyyar adawar tace Alhaji Atiku Abubakar bai mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu bukatu na sa ba, bayan sanar da cewa Atiku Abubakar ya sha kashi a zaben. PDP tayi wannan bayani ne ta bakin Kola Ologbondiyan.

Kola Ologbondiyan, wanda shi ne Sakataren yada labarai na PDP ya bayyana cewa babu abin da zai sa Atiku Abubakar ya bada wasu sharuda na musamman don kurum zai kira shugaba Buhari ya taya sa murnar lashe zaben na 2019.

KU KARANTA: Yadda su Atiku ke shirin kawowa Gwamnatin Buhari matsala a 2019

PDP ta bakin Mista Ologbondiyan, tace jam’iyyar APC ta murde zaben da aka yi Ranar 23 na Watan jiya, wanda hakan ya hana Atiku Abubakar samun nasara. Jam’iyyar adawar tace ba za ta hakura ba, har sai gaskiya tayi halin ta a Najeriya.

Haka zalika kuma PDP ta bayyana cewa ana neman kai wa Bukola Saraki, wanda shi ne Darektan yakin neman zaben Atiku Abubakar, hari bayan an zagaye ofishin sa kwannan nan. Jam’iyyar tace ana neman toshe manyan ‘yan adawan kasar.

PDP take cewa babu wasu bukatu da Atiku Abubakar yak enema a gaban shugaba Buhari illa iyaka ya garzaya kotu domin a ba sa gaskiya a zaben da aka yi inda aka tafka magudi domin a hana sa mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel