Idan akwai ‘Yan takaran da su ka fi ‘Yan Jam’iyyar APC kyau, ku zabe su – Inji Buhari

Idan akwai ‘Yan takaran da su ka fi ‘Yan Jam’iyyar APC kyau, ku zabe su – Inji Buhari

Mun ji labarin sakon bayanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a game da zaben gwamnonin jihohi da kuma ‘yan majalisar dokoki na jiha da za ayi Ranar Asabar dinnan mai zuwa a Najeriya.

Idan akwai ‘Yan takaran da su ka fi ‘Yan Jam’iyyar APC kyau, ku zabe su – Inji Buhari
Buhari ya fadawa Mutanen Najeriya su zabi wanda su ke so
Asali: Facebook

Shugaban kasa ya bayyana cewa dole jami’an tsaro da hukuma su kyale Najeriya su zabi duk wadanda su ke so. Shugaba Muhammadu Buhari a wannan karo ya sake fadakaar da mutane da su zabi ‘yan takarar kowace Jam’iyya.

Buhari yana mai cewa idan jama’a sun amince da ‘yan takarar da su ka fice daga jam’iyyar sa ta APC, su ka koma wasu jam’iyyu, to su zabe su, muddin za su kamanta masu adalci tare da yi masu gaskiya idan har su ka samu mulkin jiha.

KU KARANTA: Ai dama na hango cewa Buhari ya ci zabe ya gama inji Gwamnan Kudu

Shugaba Buhari dai ya nuna cewa bai da matsala da duk wadanda su ka tsere daga jam’iyyar APC mai mulki su ka nemi takara a wasu jam’iyyun hamayya. Shugaban kasar yace abin da yake so, shi ne ya ga an yi gaskiya a zaben na 2019.

A jawabin na shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa yana takaicin ganin an yi magudi da ha’incin zabe don haka ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu yayi aringizo ko kuma yayi amfani da ‘yan daba wajen tarwatsa zabe.

Shugaban kasan yayi wannan magana ne a wani faifen murya wanda ya shigo hannun mu a karshen makon nan. A karshen makon nan da aka shiga ne za ayi zaben Gwamnonin jihohi a fadin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel