Da hannun wasu mayan a rashin zaman lafiyar jihae Benuwe - Rundunar soji

Da hannun wasu mayan a rashin zaman lafiyar jihae Benuwe - Rundunar soji

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewar da akwai sa hannun wasu manyan mutane a Benuwe a rigingimun da jihar ke fama da su, musamman na baya bayan nan.

Manjo Janar Adeyemi Yekini, kamandan rundunar atisaye ta ‘operation whirl stroke (OPWS)’, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Makurdi, babban brnin jihar Benuwe.

Yekini ya ce irin wadannan manyan mutane da ke da hannu a rigingimun jihar ne su ka dauki nauyin hare-haren da aka kai kan wasu al’ummar jihar gabanin zaben da aka yi makon jiya.

A bayyana ya ke wasu mutane na kara rura wutar rikici a Benuwe; ba wai tsautsayi ba ne ya sa aka kai hari a kan al’ummar garin Agatu ana saura mako guda a yi zaben shugaban kasa kuma ga shi yanzu an sake kai wani harin a yayin da ya rage saura mako guda a gudanar da zaben gwamnoni,” a cewar Yekini.

Da hannun wasu mayan a rashin zaman lafiyar jihae Benuwe - Rundunar soji
Dakarun Rundunar soji
Asali: Facebook

A shekarar 2018 ne shugaba Buhari ya kaddamar da rundunar atisaye ta OPWS domin daile aiyukan ta’addanci a jihohin Benuwe, Nasarawa da Taraba.

Yekini ya kara da cewa dakarun soji sun kara kaii a atisayen da su ke yi a Loko zuwa Agatu zuwa Kwande da sauran garuruwa da ke kan iyakar jihar Benuwe domin ganin ba a kara samun kwatankwacin hare-haren da su ka afku ba a baya.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin gwamnonin APC da jam’iyya ta dakatar ya ziyarci Buhari, hotuna

Ya nuna mamakin sa bisa yadda ake daukan ran mutum a matsayin fansar na dabba.

Mohammed Abubakar, wani jami’in rundunar soji da ke jagorantar OPWS a karamar hukumar Gwer ta yamma, ya ce wasu ‘yan ta’adda na amfani da kayan soji domin aikata laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel