Daya daga cikin gwamnonin APC da jam’iyya ta dakatar ya ziyarci Buhari, hotuna

Daya daga cikin gwamnonin APC da jam’iyya ta dakatar ya ziyarci Buhari, hotuna

Da ranar yau, Lahadi, ne gwaman jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Ganawar shugabannin biyu na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan kwamitin gudanar wa (NWC) na jam’iyyar APC ya amince da dakatar da Amosun da Rochas bisa zargim su da cin amanar jam’iyya.

NWC ya bayar da shawarar korar gwamnonin biyu daga jam’iyyar.

Ana zargin Amosun da tunzura matasan da su ka hana a kaddamar da kamfen din shugaban kasa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, cikin lumana da kuma nuna goyon baya gad an takarar gwaman a jam’iyyar APM a zaben gwamnoni da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Daya daga cikin gwamnonin APC da jam’iyya ta dakatar ya ziyarci Buhari, hotuna
Amosun ya ziyarci Buhari
Asali: Twitter

Daya daga cikin gwamnonin APC da jam’iyya ta dakatar ya ziyarci Buhari, hotuna
Amosun da Buhari
Asali: Facebook

A wani labarin na Legit.ng kun je cewar Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta tabbatar da cewar a gobe, Litinin, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar godiya ga al’ummar jihar Taraba bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kujearar shugaban kasa.

Mista Aeron Atimas, kakakin jam’iyyar APC a jihar Taraba, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya na mai bayyana cewar jihar na zuciyar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Harin ‘yan daba: Gwamna Dankwambo ya tsallake rijiya da baya

A cewar Atimas, shugaban Buhari ya matukar jin dadin yadda jama’a su ka fito kwan su da kwarkwata su ka tarbe shi lokacin da ya ziyarci jihar yayin yakin neman zabe. Kazalika, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yi matukar farinciki da sakamakon zaben shugaban kasa.

Atimas ya kara da cewa shugaba Buhari zai ziyarci jihar Taraba bisa la’akari da uwar jam’iyya ta kasa ta yi a kan yiwuwar APC ta lashe aben gwamnan jihar muddin jama’a su ka samu tabbacin cewar za a cika ma su dukkan alkawuran da aka dauka bayan an ci zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel