Nasarar zabe: Buhari zai kai ziyarar godiya jihar Taraba ranar Litinin

Nasarar zabe: Buhari zai kai ziyarar godiya jihar Taraba ranar Litinin

Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta tabbatar da cewar a gobe, Litinin, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar godiya ga al’ummar jihar Taraba bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kujearar shugaban kasa.

Mista Aeron Atimas, kakakin jam’iyyar APC a jihar Taraba, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya na mai bayyana cewar jihar na zuciyar shugaban kasa.

A cewar Atimas, shugaban Buhari ya matukar jin dadin yadda jama’a su ka fito kwan su da kwarkwata su ka tarbe shi lokacin da ya ziyarci jihar yayin yakin neman zabe. Kazalika, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yi matukar farinciki da sakamakon zaben shugaban kasa.

Atimas ya kara da cewa shugaba Buhari zai ziyarci jihar Taraba bisa la’akari da uwar jam’iyya ta kasa ta yi a kan yiwuwar APC ta lashe aben gwamnan jihar muddin jama’a su ka samu tabbacin cewar za a cika ma su dukkan alkawuran da aka dauka bayan an ci zabe.

Nasarar zabe: Buhari zai kai ziyarar godiya jihar Taraba ranar Litinin
Ziyarar Buhari a jihar Taraba
Asali: UGC

Ziyarar shugaban kasa ta gobe za ta kara wa APC kwarin guiwa da farin jinni a wurin jama’a, hakan kuma zai kara ma na karkasashin samun nasara a zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na ranar Asabar, 9 watan Maris.

“A shirye mu ke tsaf domin karbar shugaban kasa a gobe, a shirye mu ke domin mu nuna wa uwar jam’iyya cewar jihar Taraba ta APC ce kuma za mu tabbatar wa da duniya hakan a zaben ranar Asabar mai zuwa, zaben da APC za ta lashe,” a cewar Atimas.

DUBA WANNAN: Harin ‘yan daba: Gwamna Dankwambo ya tsallake rijiya da baya

Da su ke mayar da martani a kan ziyarar ta Buhari, jam’iyyar PDP a jihar Taraba ta yi kira ga shugaban kasar da ya yi amfani da ziyarar da zai kai wajen jan kunnen magoya bayan jam’iyyar sa a kan salon daba da su ke amfani da shi yayin yakin neman zabe.

Inuwa Bakari, kakakin jam’iyyar PDP aTaraba, ya yi watsi da batun cewar ziyarar shugaba Buhari za ta kara wa APC farin jin a jihar.

“Idan shugaban kasa ya na so zai iya tare wa a Taraba, babu abinda zai canja, PDP za ta lashe zabe a jihar kamar yadda ta saba tun shekarar 1999,” a cewar Bakari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel