An fara kira ga APC ta raba kujerun Majalisa ga kowane Yankin Najeriya

An fara kira ga APC ta raba kujerun Majalisa ga kowane Yankin Najeriya

- Yekini Nabena yayi kira ga Jam’iyyar APC su tashi tsaye a Majalisa

- Jigon na APC yace ‘Yan adawa na kuma shirin yi masu karfa-karfa

- Nabena ya nemi Jam’iyyar APC ta kasa kujerun Majalisun Tarayya

An fara kira ga APC ta raba kujerun Majalisa ga kowane Yankin Najeriya
Nabena yace 'Yan adawa na da shirin karbe Majalisar Tarayya
Asali: Twitter

Yekini Nabena wanda shi ne mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC mai mulki na kasa yayi ikirarin cewa jam’iyyar adawa ta PDP na neman hanyar da za tayi na ganin ta karbe ragamar majalisar tarayya wannan karon.

Babban jagoran na APC ya bayyana cewa PDP na kokarin tattare manyan mukamai a majalisa duk da cewa jam’iyyar ba ta da rinjaye. Yekini Nabena ya bayyana wannan ne lokacin da yayi hira da wasu manema labarai jiya Ranar Asabar.

KU KARANTA: Jerin wadanda su ka kwallafa ran su a kujerar Majalisar Wakilai

Mista Nabena yake cewa don haka akwai bukatar APC ta kasa mukaman majalisa a wannan karo domin gudun abin da ya faru bayan zaben 2015 ya sake faruwa. A 2015, APC tayi sakaci har Bukola Saraki ya zama shugaban majalisar dattawa.

Nabena yace tuni PDP ta shirya yadda za ta kawowa gwamnati cikas ta hanyar yin keme-keme a kan mukaman majalisa. Sakataren yada labaran na APC yace PDP sun shirya wannan ne lokacin da su ke dabarun yakin neman zaben 2019.

Mista Nabena yace Bukola Saraki ne ya rika kawowa Buhari matsala a karon nan na sa na farko saboda manufar siyasar sa. Kakakin jam’iyyar ta APC yace tsayin-dakan da Buhari yayi ne ya sa PDP ta gaza rusa nasarorin gwamnatin APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel