Harin ‘yan daba: Gwamna Dankwambo ya tsallake rijiya da baya

Harin ‘yan daba: Gwamna Dankwambo ya tsallake rijiya da baya

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu ‘yan daba su ka kai wa tawagar sa farmaki tare da koma motaci guda biyu.

Dahiru Kera, Darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamanan jihar Gombe a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ne ya sanar da hakan a yau, Lahadi, 03 ga watan Maris.

Kera ya bayyana cewar ‘yan dabar sun kai wa Dankwambo harin ne a hanyar sa ta dawowa daga filin tashi da saukar jirgin sama.

A cewar Kera, ‘yan dabar da su ka kai wa gwamnan hari sun kone motoci biyu daga cikin tawagar da ke biye da shi. Jaridar Vanguard ta kara da cewa ‘yan dabar sun wuce zuwa unguwar Lafiyamo da ke kan hanyar zuwa filin jirgin sama inda su ka kona wani gidan Radiyo mai zaman kan sa, Progress FM.

Bayan kaddamar da wadannan hare-hare biyu, ‘yan dabar sun kona shaguna 8 a unguwar tare da kara kone wasu motocin biyu a unguwar Jekada Fari.

Harin ‘yan daba: Gwamna Dankwambo ya tsallake rijiya da baya
Ibrahim Hassan Dankwambo
Asali: Depositphotos

Kwamishinan ‘yan sanda, Bello Makwashi, ya tabbatar da kai harin ta bakin kakakin rundnar na jihar Gombe, Mary Malum.

Ya bayyana cewar tuni sun fara bincike a kan harin da ‘yan dabar su ka kai.

Malam Nuhu Usman, wani shaidar gani da ido, ya ce ‘yan dabar sun fara da jifan tawagar gwamnan ne kafin daga bisani su kone shaguna 8 unguwar. Ya kara da an kai jama’a da dama asibiti saboda raunukan da su ka samu.

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi irin kalar mutanen da zai bawa mukami a zango na biyu

Sai dai, manajan gidan Radiyon da aka kai harin, Alhaju Ibrahim Biu, ya zargin wasu ‘yan dabar siyasa da ke bin tawagar gwamnan da kai ma su hari. A cewar sa, “a jiya da yamma ne wasu ‘yan daba dauke da makamai da ke bin tawagar gwamna yayin dawowar sa daga filin jirgi su ka kai ma na hari.

Sun jefo duwatsu cikin gidan Radiyon mu a daidai lokacin da su ke kokarin tsallako wa zuwa cikin haraba. Nan da dan na kira kwamishinan ‘yan sanda da darektan rundunar tsaro ta farin kaya kuma sun gaggauta daukan mataki.

“Sun raunata daya daga cikin ma su gadin mu yayin harin. Abun ya matukar ba mu tsoro. Mu na godiya ga jami’an tsaro.

Da ya ke mayar da martini, Kera ya musanta cewar ‘yan dabar na tare da tawagar gwamnan ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel