Zaben Gwamnoni: Buhari zai ziyarci jihar Akwa Ibom da Imo

Zaben Gwamnoni: Buhari zai ziyarci jihar Akwa Ibom da Imo

A yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni na jihohin kasar nan a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, a yau Litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci wasu jihohi biyu a Kudancin Najeriya domin mika godiyar sa ta samun nasara.

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, a yau Litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihohin Akwa Ibom da kuma Imo da mika godiyar sa ta samun nasarar tazarce da kuma taya 'yan takarar jam'iyyar sa ta APC yakin zabe.

Shugaba Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Akwai Ibom
Shugaba Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Akwai Ibom
Asali: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gabanin ranar Asabar ta wannan mako da za a gudanar da babban zabe na gwamnoni da kuma 'yan majalisun dokoki na jiha, shugaban kasa Buhari zai kuma ziyarci jihohin Kaduna, Taraba, Sakkwato da kuma Katsina.

Kawowa yanzu ba bu wani tabbaci dangane da ababen da shugaban kasa Buhari zai aiwatar yayin ziyarar sa, sai dai binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, shugaba Buhari zai gudanar da zaman sauraron ra'ayi domin mika godiyar sa ta samun nasara tare neman goyon bayan jam'iyyar sa ta APC a lokutan zaben kujerar gwamna a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna na PDP ya sauya sheka

Ko shakka ba bu shugaban kasa Buhari ya yi nasara yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, inda ya lallasa abokin adawarsa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, kasancewar su ginshikai na jam'iyyar adawa ta PDP, shugaban kasa Buhari zai ziyarci jihohin Taraba, Sakkwato da kuma Akwa Imo domin tabbatar da nasarar jam'iyyar sa ta APC.

Duba da yanayi da harkallar al'amurra, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shine zai wakilci shugaban kasa Buhari a yau cikin birnin Uyo da misalin karfe 2.00 na Yammaci kamar yadda, Sanata Ita Enang, hadimin shugaban kasa akan al'amurran yau da kullum ya bayyana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel