Nasarar Buhari ta kwantar da hankalin Ma'aikatan NNPC - Ughamadu

Nasarar Buhari ta kwantar da hankalin Ma'aikatan NNPC - Ughamadu

Biyo bayan nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga wata Fabrairun 2019, mun samu cewa ma'aikatan kamfanin man fetur na kasa wato NNPC sun bayyana farin cikin su.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, nasarar shugaban kasa Buhari a yayin babban zabe kasa za ta yi tasirin gaske wajen habaka harkokin gudanarwa da kuma inganci na babban kamfanin man fetur na kasa wato NNPC.

Daya daga manyan jagorori na kamfanin, Mista Ndu Ughamadu, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawar sa da manema labarai a garin Abuja tare da tabbatar da yadda shugaban kasa Buhari ke ci gaba da bayar da muhimmiyar gudunmuwa wajen habakar kamfanin.

Buhari tare da shugaban NNPC na kasa, Dakta Maikanti Baru
Buhari tare da shugaban NNPC na kasa, Dakta Maikanti Baru
Asali: UGC

Mista Ughamdu ya ke cewa, kasancewar shugaban kasa Buhari Ministan man fetur Kasa, ya na ci gaba da taka muhimmiyar rawar gani wajen inganta harkokin su na gudanar wa tare da goyon baya maras yankewa.

Kazalika wani babban jagoran tsaro na kamfanin, Mista Sam Otobueze, ya ce nasarar shugaban kasa Buhari za ta yi tasirin wajen ci gaba da kasancewa da kuma dorewar kamfanin a karkashin akala ta gudanarwar gwamnatin tarayyar kasar nan.

Duba da yadda dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin sayar da kamfanin NNPC muddin ya zamto shugaban kasar Najeriya, a halin yanzu ma'aikatan kamfanin sun bayyana farin cikin su kwarai da aniyya yayin da nasara ta rinjaya ga shugaban kasa Buhari a babban zabe.

KARANTA KUMA: Hotunan Fatima Ganduje bayan shekara guda da auren ta

Jaridar Legit.ng ta ruwaito, bisa ga zayyana dalilai da suka hadar da rashin cimma manufa da kuma watsi da akidar samar da kamfanin tsawon shekaru 60 da suka gabata, tsohon Mataimakin shugaban kasa ya sha alwashin sayar da kamfanin a duk sa'ilin da ya kasance jagoran Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel