Ina sane cewa Shugaban kasa Buhari zai zarce shiyasa na bi a hankali – Inji Obiano

Ina sane cewa Shugaban kasa Buhari zai zarce shiyasa na bi a hankali – Inji Obiano

Mun ji labari Mai girma gwamna Willie Obiano, na jihar Anambra, ya bayyana cewa tuni ya gano lallai shugaba Muhammadu Buhari ne zai yi nasara a zaben shugaban kasa da aka yi cikin kwanakin nan.

Ina sane cewa Shugaban kasa Buhari zai zarce shiyasa na bi a hankali – Inji Obiano
Obiano yace ya san Buhari zai ci zabe don haka ya ajiye kayan fada
Asali: UGC

Gwamna Willie Obiano yayi wannan bayani ne ta bakin babban Sakataren sa watau James Eze. Gwamnan yace dama can ya fadawa mutanen sa cewa babu wanda zai iya tika shugaban kasa Buhari da kasa a zaben da za ayi.

James Eze yace wannan ne ya sa gwamnan na APGA ya rika kokarin jan kunnen kungiyoyin Ibo da su guji yin adawar da za ta kai su rami a wannan kato. Gwamnan yace babu hikima ga yin fito na fito da shugaba mai iko a kasar.

KU KARANTA: Ana hada mu da EFCC ne saboda in hakura da zuwa Kotu – Atiku

Gwamna Obiano ya nuna hikimar yin siyasa cikin lalama domin gudun abin da zai je ya dawo. Sakataren gwamnan ya kare matsayar da Mai gidan na sa ya dauka kwanaki, inda yace ba kowa bane ya hango abin da shi ya hango.

Mista Eze yake cewa gwamnan na jihar Anambra watau Willie Obiano yana da kaifin hangen nesa da basira, inda abin da yake nunawa mutanen sa na Ibo ya fito fili yanzu bayan shugaba Buhari ya samu zarcewa a kan karagar mulki.

Hadimin na Cif Willie Obiano, yake cewa saboda tsoron rana irin wannan ne gwamnan ya ki biyewa sauran Ibo wajen yin arba da Buhari. Wasu dai sun ta sukar gwamnan a lokacin da yaki marawa PDP baya a zaben shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel