Ya kamata ka saduda hakan nan ka rungumi sakamakon zabe – IBB ga Atiku

Ya kamata ka saduda hakan nan ka rungumi sakamakon zabe – IBB ga Atiku

Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai ritaya ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna kan nasarar da ya samu na lashe zaben kasar.

IBB ya kuma yaba ma babban abokin adawarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bisa yadda ya nuna dattako a lokacin gudanarwar zaben.

Tsohon Shugaban kasar ya kuma shawarci Atiku da ya hakura ya aminta da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar wanda ke nuna cewa shugaba Buhari yayi nasara.

Babangida ya nusar da tsohon mataimakin Shugaban kasar cewa ya kamata ya janye sannan kuma ya taya Buhari murna domin muradin kasar da kuma zaman lafiyarta, amma ba don komai ba.

Ya kamata ka saduda hakan nan ka rungumi kaddara – IBB ga Atiku
Ya kamata ka saduda hakan nan ka rungumi kaddara – IBB ga Atiku
Asali: UGC

Har ila yau tsohon Shugaban kasar ya yaba wa masu kada kuri’a wadanda su ka fito su ka jefa kuri’aunsu cikin mutunci da zaman lafiya ba tare da tashin-tashina ba.

Ya kuma yi kira ga Buhari bisa yadda ya kula da cewa zaben irin na kan-kan-kan ne, wanda ba a saba ganin kamarsa ba a kasar. Don haka sai ya bukaci da ya nemo hanyoyin da za su hada kan kasar, su kuma rage damuwar da ta afku a lokacin yakin neman zaben.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa babban limamin coci Prophet Emmanuel Omale wanda yayi hasashen nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 ya sake hasashen cewa zuwan Buhari na biyu zai amfani talakawa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Ganduje, Masari, Gaidam suka gaza cika alkawurran su na zaben Buhari

A wata hira da jaridar Nigerian Tribune, limamin cocin Divine Hand of God International Ministries yace aikinsa ne fada ma mutane abunda ya ji daga wajen Ubangiji.

Shugaban addinin yayi kira ga yan Najeriya da su yi gangami wajen mara wa shugabancin Buhari na biyu baya domin zai amfani talakawa sosai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel