Buhari ya fadi irin kalar mutanen da zai bawa mukami a zango na biyu

Buhari ya fadi irin kalar mutanen da zai bawa mukami a zango na biyu

- A jiya, Asabar, ne kungiyar mata da matasa ta shirya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari liyafa domin taya shi muranar lashe zabe

- Buhari ya ce mutane ma su kima da son cigaban Najeriya ne kawai za su mukami a gwamnatin sa

- Shugaban kasar ya yi alkawarin bawa mata da matasa mukamai a cikin sabbin nade-nade da zai yi a zangon san a biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mutane ma su kima da kishin Najeriay ne kawai za su mukamai a nade-naden da zai yi a sabuwar gwamnatin sa.

Kazalika ya yi alkawarin kara yawan mata da matasa a cikin sabbin nade-naden saboda irin muhimmiyar gudunmawar da su ka bayar wajen samun nasarar sa a zaben da aka yi a karshen makon jiya.

Ya bayyana cewar gwamnatin sa ba zata bawa mata da matasa kunya ba.

Buhari ya fadi irin kalar mutanen da zai bawa mukami a zango na biyu
Buhari
Asali: Twitter

Buhari ya yi wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi a wurin liyafar da mata da matasan jam’iyyar APC su ka shirya ma sa omin taya shi murnar samun nasarar lashe zaben kujerar shugaban kasa a karo na biyu.

Ya ce samar da taki a kan farashi mai rahusa ya kawo habakar samun amfanin gona da kuma rage yawan shigowa da kayan abinci daga kasashen ketare.

DUBA WANNAN: Zabe: An yi wa ma’aikatan mu fyade, an sace wasu – INEC

Buhari ya yi kira ga matasan Najeriya da su rungumi noma domin kawar da yunwa da samun hanyoyin dogaro da kai.

Kazalika, ya soki shekaru 16 na mulkin PDP tare da zargin su da barnatar da dumbin dukiyar kasa da Najeriya ta samu a lokacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel