Faston da yayi hasashen nasarar Buhari ya saki sabon wahayi

Faston da yayi hasashen nasarar Buhari ya saki sabon wahayi

- Prophet Emmanuel Omale ya bukaci yan Najeriya da su yi gangamin mara wa shugabancin Buhari baya a karo na biyu

- Malamin addinin yayi hasashe a baya cewa Buhari ne zai lashe zaben shugaban kasa

- Omale yace gwamnatin Buhari na biyu zai amfani talaka sosai

Babban limamin coci Prophet Emmanuel Omale wanda yayi hasashen nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 ya sake hasashen cewa zuwan Buhari na biyu zai amfani talakawa.

A wata hira da jaridar Nigerian Tribune, limamin cocin Divine Hand of God International Ministries yace aikinsa ne fada ma mutane abunda ya ji daga wajen Ubangiji.

Faston da yayi hasashen nasarar Buhari ya saki sabon wahayi
Faston da yayi hasashen nasarar Buhari ya saki sabon wahayi
Asali: UGC

Shugaban addinin yayi kira ga yan Najeriya da su yi gangami wajen mara wa shugabancin Buhari na biyu baya domin zai amfani talakawa sosai.

Omale ya kuma yi kira ga Atiku da ya yarda da sakamakon zaben inda ya bayyana hakan a matsayin wani kudiri na Allah.

KU KARANTA KUMA: Zan ba mata da matasa dama a majalisana na gaba - Buhari

A halin da ake ciki, mun ji cewa tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai ritaya ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna kan nasarar da ya samu na lashe zaben kasar.

IBB ya kuma yaba ma babban abokin adawarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bisa yadda ya nuna dattako a lokacin gudanarwar zaben.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel