An samu mutane da-dama da su ke neman fitowa takarar shugabancin Majalisa a Najeriya

An samu mutane da-dama da su ke neman fitowa takarar shugabancin Majalisa a Najeriya

Bayan zaben ‘yan majalisu da aka yi, inda jam’iyyar APC mai mulki ta tabbatar da rinjayen ta, mun fahimci cewa yanzu APC ta fara tunanin wadanda za su rike mata bangaren majalisar wakilai a Najeriya.

An samu mutane da-dama da su ke neman fitowa takarar shugabancin Majalisa a Najeriya
‘Yan Majalisun APC sun fara hangen kujerar Dogara a 2019
Asali: Twitter

A zaben da aka yi a Najeriya, APC ta samu ‘yan majalisu fiye da 220 a majalisar wakilai na tarayya cikin ‘yan majalisu 360 na kasar. PDP mai adawa kuma mai ‘yan majalisu sama da 100 za su zama ‘yan hamayya ne wannan karo.

Hakan na nufin Yakubu Dogara na PDP duk da ya ci zabe, zai rasa kujerar sa tun da ya sauya sheka daga APC. Yanzu dai ana tunani cewa kujerar majalisar za ta fito ne daga kasar Yarbawa ko tsakiyar Najeriya a cikin ‘Yan jam'iyyar APC.

Daga cikin wadanda ake tunani za su iya kawo kujerar akwai:

1. Femi Gbajabiamila

Tun a 2015 ne jam’iyyar APC ta so ace Honarabul Femi Gbajabiamila ne ya zama shugaban majalisar wakilai.’Dan majalisar na mazabar Surulere I ya dade a majalisa (tun 2003) kuma ya san aiki nesa ba kusa ba.

KU KARANTA: APC na tunanin wadanda za su rike Majalisar Dattawa bayan Saraki

2. Ahmad Idris Wase

Daily Trust ta rahoto cewa Hon. Ahmad Wase wanda yake majalisa tun 2007 yana hangen kujerar Yakubu Dogara a majalisar nan da za a kafa. ‘Dan majalisar na Yankin Filato yana da kwarewa kuma yana da jama’a.

3. Babangida Ibrahim

Masu nazarin siyasa sun ce Hon. Babangida Ibrahim, ya fara sa ran samun kakkain kujerar majalisar wakilai. Sai dai B. Ibrahim zai iya samun matsalar cin ma burin sa ganin cewa ya fito ne daga jihar Katsina.

4. Mohammed T. Munguno

Saura kiris Mohammed Tahir Monguno ya zama mataimakin shugaban majalisa a 2015. Munguno wanda ya shafe wa’adi 3 a majalisa ya rasa kujerar ne bayan Femi Gbajabiamila ya sha kasa. Munguno ya fito ne daga Borno.

5. Abdulrazal Namdas

Wani ‘dan majalisa da yake harun kujerar Yakubu Dogara a wannan majalisar shi ne Razaq Namdas, wanda shi ne mai magana da yawun ‘yan majalisun a yanzu. Namdas ya fito ne daga jihar Adamawa a jam'iyyar APC.

6. Umar Bago

Wani wanda ake tunani yana iya kawo kujerar a 2019 shi ne Honarabul Umar Bago na jihar Neja. ‘Dan majalisar na Chanchaga yana cikin manyan taran Rt. Hon. Yakubu Dogara a da, kuma yana cikin masu yi wa APC biyayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel