Zabe: An yi wa ma’aikatan mu fyade, an sace wasu – INEC

Zabe: An yi wa ma’aikatan mu fyade, an sace wasu – INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta ce an sace wasu daga cikin ma’aikatan ta tare da yi wa wasu fyade yayin gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da aka yi a karshen makon jiya.

“Bayan cin zarafin ma’ikatan mu tare yi masu baraxana, an sace wasu, an yi wa wasu fyade,” a cewar kwamishin yada labarai da wayar da kan ma su zabe, Festus Okoye, a cikin wani jawabi da ya fitar ranar juma’a.

Sannan ya cigaba da cewa, “Mu na yi wa ‘yan uwa da dangin ma’aikatan mu na wucin gadi ta’aziyyar ‘yan uwan su da su ka rasa ran su yayin gudanar da aikin su.”

INEC ta kamala shiri domin ganin ba a sake samun afkuwar irin matsalolin da aka fuskanta a zaben da za ta gudanar na gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi ranar 9 ga watan Maris.”

An samu barkewar rikici da ta jawo tsaiko da asarar rayuka a zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu, lamarin da ya sa ake zargin an tafka magudi a irin wuraren da rikicin ya shafa, musamman a kudancin Najeriya.

Zabe: An yi wa ma’aikatan mu fyade, an sace wasu – INEC

Cibiyar tattara wa da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa
Source: Original

Kazalika, Okoye ya yi tir da halayyar da wasu jami’an tsaro su ka nuna yayin zaben tare da bayyana cewar INEC za ta tattauna matsalar da babban sifeton rundunar ‘yan sanda na kasa.

DUBA WANNAN: Rana zafi, inuwa kuna: Sanatocin APC sun fara huro wa Saraki wuta

A cewar Okoye, “duk da mun yaba da gudunmawar da jami’an tsaro su ka bayar wajen ganin an yi zabe an gama cikin lumana, dole mu yi tir da halayyar da wasu jami’an tsaro su ka nuna a wasu jihohi.

“INEC ta damu matuka a kan abinda irin wadannan jami’an tsaro su ka aikata kuma za mu tattauna da babban sifeton rundunar ‘yan sanda domin ganin yadda za a gyara da kuma ganin an hana hakan sake faruwa a zabe na gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel