Akwa Ibom: Kotu ta hana a mikawa ‘Dan takarar da ya ci zabe takardar shaida

Akwa Ibom: Kotu ta hana a mikawa ‘Dan takarar da ya ci zabe takardar shaida

Alkalin wani babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya hana hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya watau INEC ta bada takardar samun nasara a zaben da aka yi ga wani ‘dan takarar Sanata.

Akwa Ibom: Kotu ta hana a mikawa ‘Dan takarar da ya ci zabe takardar shaida
INEC za ta dakata da mikawa wanda ya ci zabe a Akwa Ibom satifiket
Asali: Depositphotos

Alkali mai shari’a Valentine Ashi na babban kotun tarayya da ke cikin Garin Abuja ya nemi INEC ta dakatar da bada takardar satifiket na nuna shaidar cin zabe ga masu neman Sanatan Arewa maso Yammaci jihar Akwa Ibom.

A Ranar Juma’ar nan da ta gabata ne kotu ta dauki wannan mataki bayan Sanatan da ke kan kujerar Sanata na Yankin watau Godswill Akpabio ya nemi kotu ta sake duba lamarin zaben da ya sha kasa hannun ‘dan takarar PDP.

KU KARANTA: Lissafin APC ya koma kan wadanda za su rike Majalisar Dattawa

Bayan an yi zabe ne wani Lauya Daniel Idoko ya shigar da kara yana korafi game da zaben da tsohon Sanata Godswill Akpabio ya rasa. Sanata Godswill Akpabio wanda ya koma APC yanzu ya sha kayi ne a hannun ‘dan takarar PDP.

Wasu masu neman takarar Sanata a APC a Kudancin Najeriya sun sha kashi a zaben ‘yan majalisun tarayya da aka yi. Yanzu dai APC tana da rinjaye na Sanatoci 60, yayin da PDP mai adawa ta ke da 40.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel