Ohaneze, Afenifere, PANDEF sun ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa

Ohaneze, Afenifere, PANDEF sun ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa

Kungiyoyin Ohaneze Ndigbo, Afenifere, Pan Niger Delta Forum (PANDEF) da dattawan Arewa sun ki amincewa dasakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu inda suka ce lallai shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi nasara ne ba bisa ka’ida ba.

Cif John Nwodo wanda ke jagorantar Ohamez Ndigbo, Ango Abdullahi da ke jagorantar kungiyar dattawa arewa, Ayo Adebanjo na Afenifere da Edwin Clark na PANDEF dai sun nuna goyon bayansu ne ga Atiku koda dai ya sha kashi a hannun Buhari.

Yayinda suke sake duba manyan abubuwan da suka kunshi zaben, tsari da gudanarwar zaben da kuma yadda aka sanar da sakamakon zaben, kungiyoyin sun yi zargin cewa akwai maigida a zaben.

Ohaneze, Afenifere, PANDEF sun ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa
Ohaneze, Afenifere, PANDEF sun ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa
Asali: Twitter

Dattawan dai sun shawarci Atiku da ya shigar da kara kotu domin a bi masa hakkinsa.

Kungiyoyin sun yi kira ga yan Najeriya da su tsaya tsayin daka don tabbatar da ganin an nada sahihin Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Zan ba mata da matasa dama a majalisana na gaba - Buhari

Ba tare da bata lokaci ba jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta mayar da martani, cewa matsayar kungiyar bai da amfani bayan yan Najeriya sun gama magana a lokacin zabe.

A lokacin zabe kungiyar ta marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar baya “bisa kudirin cewa ya fahimci abubuwan da kasar ke bukata a wannan mawuyacin yanayi."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel