Ba mu yi na’am da matakin da aka dauka game da su Uguru Uguru ba – Eton John

Ba mu yi na’am da matakin da aka dauka game da su Uguru Uguru ba – Eton John

Mun ji labari daga wata jaridar kasar nan cewa wani bangare na jam’iyyar APC na taware a jihar Cross River, ya bayyana cewa ba su amince da dakatar da wasu ‘ya ‘yan su da uwar jam’iyyar tayi ba.

Ba mu yi na’am da matakin da aka dauka game da su Uguru Uguru ba – Eton John
Mutanen Uguru Uguru sun maidawa Majalisar Oshimohole raddi
Asali: UGC

Godwin Eton john, wanda shi ne shugaban wasu ‘yan taware na bangaren APC a jihar, yayi watsi da korar Fasto Usani Usani tare da wasu mutum 3 na jam’iyyar. Eton john, yayi wannan jawabi ne ta bakin babban Sakataren sa.

Sakataren na ‘yan taware a jihar ta Cross River watau Francis Ekpenyong, ya fitar da bayani jiya inda yace majalisar NWC na APC ba ta da hurumin dakatar da Usani Usani ba tare da ta kira sa ya kare korafin da ke kan sa ba.

KU KARANTA: Buhari bai jin dadin abin da wasu manyan APC su ke yi

Mista Francis Ekpenyong ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da manema labarai a jihar inda yace bai dace APC kurum ta yanke wannan mataki daga Abuja, ba tare da zuwa jihar ta gudanar da binciken da ya dace ba.

APC tana zargin ministan na Neja-Delta da laifin yi wa jam’iyya zagon-kasa. Tuni dai wannan bangare na APC da ta ke tare da ministan ta karyata wannan zargi inda tace su Hilliard Eta, da Ndoma-Egba ne ke kawo APC cikas.

‘Yan tawaren sun soki yadda Adams Oshiomhole da majalisar sa su ka hada kai da Owan Enoh da kuma John Ochala wajen dakatar da Usani Usani wanda yake ikirarin cewa shi ne ‘dan takarar gwamnan na APC a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel