Zan ba mata da matasa dama a majalisana na gaba - Buhari

Zan ba mata da matasa dama a majalisana na gaba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zai yi duba ga bukatar ba mata da matasa dama a majalisarsa ya gaba.

Ya bayyana hakan ne a daren ranar Asabar, 2 ga watan Maris lokacin wata walimar taya murna da kwamitin kamfen din shugaban kasa na mata da matasa suka shirya a fadar shigaban kasar da ke Abuja Wanda gidan talbijin din NTA ta haska kai tsaye.

Cikin raha shugaban kasar ya kuna bayyana cewa zai kare ra’ayin tsoffin mutane kamar shi.

Zan ba mata da matasa dama a majalisana na gaba - Buhari
Zan ba mata da matasa dama a majalisana na gaba - Buhari
Asali: Depositphotos

Yayin kafa sabuwar majalisa, shugaban kasar yace zai so ba mutane masu mutunci mukamai domin su taimaka mas wajen karfafa nasarorin da ya samu ta fannin yaki da cin hanci da rashawa, habbaka tattalin arziki, tsaro da kuma rage dogaro da mai a kasar.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a jiya Asabar ya kaddamar da kungiyar lauyoyin sa domin kalubalantar sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

KU KARANTA KUMA: EFCC: Ba zan yarda cewa Shugaba Buhari ya tika ni da kasa ba – Atiku

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kungiyar lauyoyin bisa jagorancin Dakta Livy Uzoukuwa (SAN), za ta kalubalanci sakamakon babban zaben ta hanyar neman kotu ta yi watsi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel