Rana zafi, inuwa kuna: Sanatocin APC sun fara huro wa Saraki wuta

Rana zafi, inuwa kuna: Sanatocin APC sun fara huro wa Saraki wuta

Mambobin jam’iyyar APC a majalisar dattijai sun shaidawa majiyar mu cewar sabon shugabancin majalisar da za su kafa a watan Yuni zai binciki shugabancin majalisar da Sanata Abubakar Bukola Saraki ya shafe shekaru hudu ya na yi.

Sanatocin na jam’iyyar APC da su ka yi nasara sake lashe zaben da aka yi satin da ya gabata sun bayyana cewar shugabancin majalisar zai binciki yadda Saraki ya yi amfani da kudaden da majalisar ke da su a tsawon shekaru hudu da ya yi ya na jagoranci.

Saraki ya zama shugaban majalisar dattijai ne a shekarar 2015 a cikin wani yanayi mai tsanani da rudani saboda takun saka da ke tsakanin sa da fadar shugaban kasa da shugabancin jam’iyyar APC.

Daga bisani Saraki ya fice daga jam’iyyar APC ya koma tsohuwar jam’iyyar sa, PDP, da ya mulki jihar Kwara na tsawon shekaru 8 a cikin ta.

Rana zafi, inuwa kuna: Sanatocin APC sun fara huro wa Saraki wuta
Saraki
Asali: Depositphotos

Sai dai, Saraki, ya sha kaye a zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya da aka gudanar a makon jiya, lamarin da ya kawo karshen zaman sa a majalisar dattijai.

Wani daga fitattun sanatocin APC ya sanar da majiyar mu cewar, “akwai yiwuwar mu binciki Saraki. Mun san cewae zai kokarin ganin ya kafa magajin sa wanda ba zai bincike shi ba. Akwai yiwuwar zai goyi bayan wanda ya san ya na da kusanci da shi domin ya zama sabon shugaban majalisar

“Amma maganar gaskiya shine akwai dalilai da hujjoji na binciken Saraki kuma za mu tabbatar mun matsa lamba an bincike shi, musamman a kan laifuka da su ka shafi yadda ya yi amfani da kasafin kudin majalisa a cikin shekaru hudu da su ka gabata,” a cewar wani Sanata da ya bukaci a boye sunan sa.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari: Kwamitin sulhun Abdulsalam ya gana da Atiku da Obi

Kazalika wani Sanatan da bai yarda a ambaci sunan sa bay a kara da cewa, “har yanzu Saraki bai hakura ba don kuwa ya na nan ya na kokarin ya kafa wanda zai zama sabon shugaban majalisar dattijai. Burin sa shine jam’iyyar PDP ta cigaba da shugabancin majalisar dattijai.

Ya na tuntubar sanatocin APC da na PDP domin ganin ya kafa na kusa da shi ya zama shugaban majalisar dattijai, sai dai za mu tabbatar da cewar duk wani mai kusanci da Saraki bai samu wata kujerar shugabanci daga cikin kujerun shugabannin majalisar dattijai ba.”

Da aka tuntubi Yusuph Olaniyonu, mai taimaka wa Saraki a bangaren yada labarai, ya ki cewa komai a kan wannan batu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel