‘Yan Majalisun APC sun soma sa ido a kan mukamin Bukola Saraki

‘Yan Majalisun APC sun soma sa ido a kan mukamin Bukola Saraki

Daily Trust ta rahoto cewa yanzu idanun ‘yan majalisa ya tattara zuwa ga wanda zai zama shugaban Sanatoci, bayan an kammala zaben majalisar tarayya a Najeriya, ganin cewa Bukola Saraki ya sha kasa.

‘Yan Majalisun APC sun soma sa ido a kan mukamin Bukola Saraki
Sanatoci na rububin wanda zai gaji kujerar Bukola Saraki
Asali: UGC

Nan da wani lokacin kadan ne za a nada sababbin shugabanni a majalisar tarayyar Najeriya. Wadanda ake ba manyan mukamai su ne wanda su ka dade a cikin majalisar. Yanzu dai APC ta ci Sanatoci 64, PDP kuma ta na da 40 rak.

Ana tunani shugaban majalisar dattawan zai fito ne daga yankin Arewa ta gabas ko tsakiya ko kuma can cikin kudu maso kudancin Najeriya. Daga cikin masu harin kujerar shugaban majalisar dattawa a APC wannan karo dai akwai:

KU KARANTA: 2019: Mun kashe Saraki murus a siyasar Kasar nan Inji Oshiomhole

1. Sanata Ahmad Lawan (Yobe APC)

2. Sanata Mohammed Ali Ndume (Borno APC)

3. Sanata Mohammed Danjuma Goje (Gombe APC)

4. Sanata Abdullahi Adamu (Nasarawa APC)

Kamar yadda mu ka ji, Sanatocin APC da su ka dawo majalisa daga Kudu maso kudancin Najeriya, ba su nuna sha’awar su game da kujerar ba. Sai dai watakila su nemi mataimakin shugaban majalisar, a yadda abubuwa ke tafiya.

Mohammed Ali Ndume ya zama Sanata ne tun 2011 bayan y abar majalisar wakilai kuma yana cikin manyan Sanatoci kuma babban yaron jam’iyyar APC a yanzu. Tsohon gwamna Danjume Goje yana cikin masu neman wannan kujera.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta taso tsohon shugaban kasa Obasanjo a gaba

Sanata Ahmad Lawal ya zo majalisa ne tun 1999, inda a 2007 ya zama Sanata. Lawan yana cikin wadanda ake tunani su ke kan gaba-gaba wajen samun kujerar shugaban majalisar dattawa saboda shirin da yake yi da wasu manya na APC.

Sanata Abdullahi Adamu wanda ya zo majalisa a 2011 bayan ya gama gwamna a Nasarawa yana cikin wadanda ke harin kujerar ta Bukola Saraki na kusa da shi. Sanatocin APC a Kudu su ne Francis Alimekhena da Ovie Omo-Agege.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel