Abubuwan da wasu ke yi a Jam’iyyar APC ba yayi wa Buhari dadi – Inuwa Abdulkadir

Abubuwan da wasu ke yi a Jam’iyyar APC ba yayi wa Buhari dadi – Inuwa Abdulkadir

Inuwa Abdul-Kadir, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai mulki na yankin Arewa maso yamma, yayi wata hira da ‘yan jarida inda ya bayyanawa jama’a halin da APC ta ke ciki.

Abubuwan da wasu ke yi a Jam’iyyar APC ba yayi wa Buhari dadi – Inuwa Abdulkadir
Abdulkadir yace APC ba za ta wargaje idan Buhari ya tafi ba
Asali: Twitter

Alhaji Inuwa Abdulkadir yayi tir da halin da APC ta shiga a jihar Ogun inda har ta kai a jefi tawagar shugaban kasa lokacin kamfe. Kwanan nan ne dai jami’an tsaro su ka iya kama wadanda ake zargi da wannan mugun aiki.

Abdulkadir yake cewa shugaban kasa Buhari bai ji dadin abin da ya auku a irin su jihar Ogun ba, indaa jam’iyyar da ke mulki ta ke cikin rikici. Wannan ya sa shugaban kasar ya fadawa jama’a su zabi duk wanda su ke so a zaben.

Babban Jagoran na jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya yace shugaan kasar yayi daidai da yayi kira ga mutane su zabi ‘dan takarar da su ke zo. Abdulkadir yake ganin cewa wasu ne su ke ta kakabawa jama’a ‘yan takara a APC.

KU KARANTA: Wani Shehi yayi wa Buhari addu’a bayan ya lashe zaben 2019

Inuwa Abdulkadir yace idan har babu adalci wajen zaben ‘dan takara a jam’iyyar APC, dole za a samu rabuwar kai kamar yadda ake gani a wasu jihohi, inda wani mutum guda kurum zai kinkimo wanda yake so ya mika masa tuta.

Sai dai wannan rikici ba zai shafi APC nan gaba ba sosai inji jigon jam’iyyar. Abdulkadir yana ganin cewa babu abin da zai sa APC ta ruguje idan Buhari ya gama mulkin sa a 2023 ba, domin kuwa jam’iyya ta zarce wani ‘dan siyasa.

A hirar da aka yi da Inuwa Abdulkadir, ya nuna inda ya sha ban-ban da manyan APC musamman a game da rikicin cikin gida da ake yi. Sannan kuma yace APC ba ta da hurumin da za ta rika yi wa ‘yan majalisa katsaladan a aikin su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel