Babu dan bautar kasa ko daya da ya rasa ransa a zaben 23 ga Fabrairu - NYSC

Babu dan bautar kasa ko daya da ya rasa ransa a zaben 23 ga Fabrairu - NYSC

Daraktar yada labarai ta hukumar, Adenike Adeyemi ce ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, jiya Asabar a Abuja, mako guda kafin zaben gwamnoni da 'yan majalisar dokoki da za a yi a ranar 9 ga watan Maris.

Daraktar ta kara da cewa,babu wani dan bautar kasa ko guda daya da ya rasa ransa a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya da aka gudanar a makon da ya gabata.

A ta bakin daraktar, "Ba za mu tura 'yan bautar kasa jihohi ko cibiyoyin da muke da rahoton akwai matsalar tsaro ba a zaben 9 ga watan Maris kasancewar akwai hasashen cewa zaben na iya zuwa da tashe-tashen hankula."

Misis Adenike ta ci gaba da cewa, hukumar tasu bata tura 'yan bautar kasa wuraren da ke da matsalar tsaro don gabatar da ayyukan hidimar kasa na farilla, balle ma har su tura su aikin zabe wanda ba wajibinsu bane.

"Akwai labarai da ke zagayawa a kafafen sadarwa musamman ma na yanar gizo, inda ake cewa wai wasu 'yan bautar kasa sun rasa rayukansu a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya na ranar 23 ga watan Fabrairu. Gaskiyar magana ita ce babu wanda ya rasa ransa a wajen aikin zabe."

"Ko'odinatan hukumar NYSC na jihar Rivers ya yi karin haske kan rade-radin da ake yi na cewar wasu 'yan bautar kasa sun mutu a jihar."

A cewar Ko'odinatan, "An samu hatsaniya da rikice-rikice a nan da can a jihar Rivers, amma babu wani dan bautar kasa ko guda daya da ya rasa ransa."

"Kafin NYSC ta yarda ta bada 'ya'yanta aiki, sai da hukumar NYSC da ta INEC suka sanya hannu akan wata yarjejeniya na cewa INEC za ta tabbatar da walwala da tsaron 'yan bautar kasa."

"Sai da INEC ta tabbatar mana nawa za ta biya kowane dan bautar kasa da kuma yadda za ta biya shi kai tsaye ba tare da mun shiga cikin harkokin biyan ba," inji Misis Adenike."

Ta ci gaba da cewa, mu daga namu bangaren za mu saka ido mu tabbatar da cewa INEC ta cika dukkan alkawuran da ta dauka na tsaro da walwalar 'yan bautar kasa.

Ta kara da cewa, bai zama dole ga kowane mai bautar kasa ya yi aikin zabe ba in har ba shi da bukatar haka. A saboda haka duk wani dan bautar kasa da aka gani yana aikin zaben, to, shi ya yi niyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel