EFCC: Ba zan yarda cewa Shugaba Buhari ya tika ni da kasa ba – Atiku

EFCC: Ba zan yarda cewa Shugaba Buhari ya tika ni da kasa ba – Atiku

Babban Abokin hamayyar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da aka yi a Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana dinbin mabiyan sa cewa ba zai bari abin da ya faru a zaben bana ya tafi a iska ba.

EFCC: Ba zan yarda cewa Shugaba Buhari ya tika ni da kasa ba – Atiku
Hukumar EFCC ba za su sa in karaya in hakura da murde zabe ba - Atiku
Asali: Depositphotos

‘Dan takarar na jam’iyyar adawa, yace babu abin da zai sa ya saduda, yayi na’am da kayin da ya sha a zaben shugaban kasa. Atiku yayi maganar na ne bayan an ji labarin cewa hukumar EFCC ta cafke wani Surukin sa jiya Asabar.

Mai magana da yawun bakin tsohon mataimakin shugaban kasar, yake cewa EFCC mai kula da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta kama Alhaji Babalele Abdullahi ne saboda Atiku ya amince da shan kayi a hannun Buhari.

KU KARANTA: Abubuwan da za su faru yanzu bayan da Buhari ya zarce a 2019

Paul Ibe a jawabin na sa yake cewa wannan lamari da ya auku ba zai sa Atiku Abubakar yayi na’am da sakamakon zaben na 2019 ba, inda yace bai da kuma niyyar kiran shugaban kasa Buhari da ya samu nasara domin taya sa murna.

Atiku dai ya tabbatar da cewa an kama Abdullahi Babale ne jiya a garin Abuja inda aka tasa shi gaba tare da wani Lawan Ayuba har su ka rubuta jawabi a gaban hukuma. Har yanzu dai hukumar tayi gum game da tsare Surukin na Atiku.

Kamar dai yadda mu ka samu labari, Iyalin ‘dan takarar shugaban kasar sun koka da barazanar da su ke fuskanta daga halin hukuma. Alhaji Abdullahi Babale shi ne mai kula da duk kamfanonin Atiku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel