Allura-ta-tono-galma: EFCC za ta fara binciken gwamnatin Obasanjo

Allura-ta-tono-galma: EFCC za ta fara binciken gwamnatin Obasanjo

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu suna nuni ne da cewa hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta fara tattara bayanai domin soma bincikar kudaden da aka fidda domin gyaran wutar lantarki lokacin gwamnatin Obasanjo.

Kamar dai yadda muka samu, kudaden da gwamnatin ta fitar a wancen lokacin domin aiwatar da wasu kwangilolin gina tashoshin samar da wutar lantarkin sun kai kimanin dala bilyan 16 daga 1999 zuwa 2007, wato lokacin mulkin Obasanjo.

Allura-ta-tono-galma: EFCC za ta fara binciken gwamnatin Obasanjo
Allura-ta-tono-galma: EFCC za ta fara binciken gwamnatin Obasanjo
Asali: Facebook

KU KARANTA: Cacar baki ta barke tsakanin Okorocha da Oshiomhole

Legit.ng Hausa ta samu cewa a dan bayanan da hukumar ta EFCC ta soma tattarawa, ana zaton hukumar za ta tuhumi mutane kusan 150 akan kudin a gaban kotu nan ba da dadewa ba.

Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta samu amincewar Shugaba Buhari akan wannan aikin.

A wani labarin kuma, Babban malamin addinin nan na kirisa mai da'awar Annabta watau Udoka Daniel Okechukwu dake zaune a jihar Anambra da yayi hasashen cewa dan takarar shugabancin kasa a PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe zaben 2019 ya sake magana.

Fasto Udoka ya bayyana cewa duk da dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta bayyana akasin abun da shi ya hasaso amma dukkan alkaluman sa na cigaba da nuna cewa Atiku din ne dai ya lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel