Zaben 2019: Iya yadda muka tsoma hannun mu a cikin zabukan da aka yi - Sojin Najeriya

Zaben 2019: Iya yadda muka tsoma hannun mu a cikin zabukan da aka yi - Sojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Asabar ta bayyana cewa ta yi aiki ne da dokokin zabe da kuma na Najeriya da aka shimfida musamman ma a wajen tsoma hannuwan su a cikin zabukan da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Wannan dai na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar rundunar ta sojojin ta fitar dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'ar ta Kanal Sagir Musa da kuma ya rarrabawa manema labarai a Abuja, babban birnin tarayya.

Zaben 2019: Iya yadda muka tsoma hannun mu a cikin zabukan da aka yi - Sojin Najeriya
Zaben 2019: Iya yadda muka tsoma hannun mu a cikin zabukan da aka yi - Sojin Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Mai da'awar Annabtar da yayi hasashen faduwar Buhari zabe ya sake magana

Legit.ng Hausa ta samu cewa a cikin sanarwar, rundunar ta kuma musanta zargin da aka yi wasu jami'an ta na harbin wasu masu zabe farar hula a wasu sassan kasar ranar zabe.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a yayin zaben musamman ma a kafafen sadarwar zamani, an yi ta yada faya-fayan bidiyoyi da kuma wasu lokutta ma hotuna na sojojin suna gallazawa masu zabe wanda hakan ya jaza cece-kuce.

Jahohin da aka zargi sojojin da yin katsalandan a lokutan zaben suna hada ne da Ribas, Legas da kuma Delta dukkanin su a kudancin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel