'Yan bindiga sun bude wuta ga tawagar dan takarar majalisar SDP, hotuna

'Yan bindiga sun bude wuta ga tawagar dan takarar majalisar SDP, hotuna

Wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun kai hari ga tawagar yakin neman zaben dan takarar majalisar jihar na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) Ebenezer Adeniyan a Akure babban birnin jihar Ondo.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a ranar Juma'a a kusa da Oke Aro na garinn Akure yayin da suke hanyarsu ta ziyarar wasu mazabu.

Dan takarar na SDP, wanda dan jarida ne da ke aiki da 'Trace News Magazine' yana takarar kujerar wakili na mazabar Akure ta Kudu II ne a majalisar jihar Ondo.

'Yan bindiga sun kai dan takarar majalisar SDP hari
'Yan bindiga sun kai dan takarar majalisar SDP hari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari

An gano cewa 'yan daban sun lalata wasu motocci ne da ke cikin tawagar kamfen din sannan suka rika harbe-harbe da bindiga domin tarwatsa tawagar yakin neman zaben.

Daya daga cikin wadanda suke cikin tawagar yakin neman zaben na Adeniyan ya tabbatar da harin.

'Yan bindiga sun kai dan takarar majalisar SDP hari
'Yan bindiga sun kai dan takarar majalisar SDP hari
Asali: Twitter

"Muna gudanar da yakin neman zaben mu a gundumomin da ke mazabar mu. Bayan mun kammala sai muka nufi Oke Aro domin mu gana da wani abokin siyasar mu.

"A hanyar mu ta dawowa sai muka tsaya da mahadar hanya da Abiodun domin mu gaishe da wasu shugabanin unguwar.

"Muna shirin tafiya sai wasu mutane uku wadanda suka rufe fuskokinsu suka nufo mu daga tsallaken titi suka fasa gilashin gaban babban motar mu.

"Sun harba harsashi a gilashin daya daga cikin motoccin kamfen din mu amma jaruman unguwar suka taru suka fatatake su."

A yayin da ya ke tsokaci a kan harin, Adeniyan ya yi girgiza a kan harin da aka kaiwa motoccin kamfen dinsa.

Ya ce an sanar da 'yan sandan na B Division ta jihar Ondo a garin Akure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel