Gwamna El-Rufai ya kai ziyara garin Karamai da aka hai hari, hotuna

Gwamna El-Rufai ya kai ziyara garin Karamai da aka hai hari, hotuna

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ziyarci garin Karamai da ke karamar hukumar Kajuru inda aka kai sabon hari kuma aka kashe mutane da dama tare da kone gidaje.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa gwamnan ya ziyarci kabarin da aka birne mutane 15 a garin bayan harin da aka kai a ranar Talata 27 ga watan Fabrairu.

"Abin bakin ciki ne mutanen da suka dade suna zaune lafiya tare kwatsam sun juya suna kashe junansu," inji shi.

A cewar gwamnan, ya zama dole a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Kajuru da Kachia.

Ya yi kira ga mazauna garuruwan da shugabanin addini su hada kai wurin yin tir da kashe-kashen kuma ya kira shugabanin al'umma su rika koyar da mabiyansu zaman lafiya.

Gwamnan ya kuma yi gargadi a kan daukan doka a hannu inda ya ce hukumomin tsaro suna gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata harin domin a hukunta su.

Sarkin Karamai, Mr Maika Musa ya bayyana damuwarsa a kan hare-haren kuma ya yi kira da gwamnati ta dauki matakin magance lamarin.

Gwamna El-Rufai ya kai ziyara garin Karamai da aka hai hari, hotuna
Gwamna Nasir El-Rufai tare da jami'an tsaro yayin da ya kai ziyara garin Karamai da ke karamar hukumar Kajuru
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari

Gwamna El-Rufai ya kai ziyara garin Karamai da aka hai hari, hotuna
Gwamna El-Rufai da tawagarsa yayin da ake zagawa da su wuraren da aka kai hare-hare a garin Karamai
Asali: Twitter

Gwamna El-Rufai ya kai ziyara garin Karamai da aka hai hari, hotuna
Gwamna Nasir El-Rufai yayin da ya ziyarci kabarin da aka birne mutanen da suka rasu sakamakon harin Karamai
Asali: Twitter

Gwamna El-Rufai ya kai ziyara garin Karamai da aka hai hari, hotuna
Gwamna El-Rufai tare da tawagarsa yayin da suka addu'o'in samun rahama ga mutanen da aka kashe a rikicin garin Karamai
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel