Yanzu yanzu: Yan ta'adda sun sake kai sabon hari a Kaduna, sun kashe mutane 5

Yanzu yanzu: Yan ta'adda sun sake kai sabon hari a Kaduna, sun kashe mutane 5

- Wasu 'yan ta'adda sun kai sabon hari a kauyen Sabon Sara da ke garin Kidendan da ke karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyar

- Harin ya faru ne da misalin karfe 1:45 na ranar Asabar bayan da 'yan ta'addan suka shiga cikin kauyen tare da harbin kan mai uwa da wabi

- Shugaban karamar hukumar Giwa, Abubakar Shehu Giwa ta bakin sakataren karamar hukumar Usman Ismail ya tabbatar da faruwar kai harin

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu yanzu na nuni da cewa wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar, sun kai sabon hari a kauyen Sabon Sara da ke cikin garin Kidendan da ke karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyar.

Harin ya faru ne da misalin karfe 1:45 na ranar Asabar bayan da 'yan ta'addan suka shiga cikin kauyen tare da harbin kan mai uwa da wabi.

Sai dai har yanzu, babu wani tabbaci kan yadda harin ya kasance, amma wani mazaunin garin wanda ya bayyana sunansa da Malam Yahaya ya ce akalla mutane bakwai ne suka samu raunuka, kuma an kaisu asibitin Zaria.

KARANTA WANNAN: Babu tantama: Yan Nigeria sun sake zabar shugaban kasa mai gaskiya - Ribadu

Yanzu yanzu: Yan ta'adda sun sake kai sabon hari a Kaduna, sun kashe mutane 5
Yanzu yanzu: Yan ta'adda sun sake kai sabon hari a Kaduna, sun kashe mutane 5
Asali: Twitter

Wadanda suka rasa rayukansu sune; Lawal, Ibrahim, Umar, Lawal da kuma Tukur. Yayin da wadanda suka jikkata sun hada da Rabilu, Sani, Mohammadu da kuma Malam Aminu.

Shugaban karamar hukumar Giwa, Abubakar Shehu Giwa ta bakin sakataren karamar hukumar Usman Ismail ya tabbatar da faruwar kai harin ga manema labarai ta wayar tarho.

A hannu daya kuwa, da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya yi alkawarin yin bayani kan harin, amma har zuwa kammala rubuta wannan labarin bai sake kiran wayar ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel