Babu tantama: Yan Nigeria sun sake zabar shugaban kasa mai gaskiya - Ribadu

Babu tantama: Yan Nigeria sun sake zabar shugaban kasa mai gaskiya - Ribadu

- Malam Nuhu Ribadu, ya ce 'yan Nigeria sun sake zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ba zai sayar da kadarorin da kasar ta mallaka ba

- Ribadu ya bukaci tawagar yakin zaben da ke karkashin sa da su sake zage damtse wajen gudanar da ayyukanta a zabukan gwamnoni da 'yan majalisun dokoki

- Ya bayyana cewa Buhari zai bukaci zabukan gwamnoni da 'yan majalisun dokoki domin ba shi damar gudanar da ayyukan ci gaba a kasar ba tare da tsaiko ba

Daraktan kwamitin yakin zabe na lunguna da sakuna karkashin ofishin yakin zaben shugaban kasa na APC, Malam Nuhu Ribadu, ya ce 'yan Nigeria sun sake zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya kasance mutum adali, mai gaskiya kuma wanda ba zai sayar da kadarorin da kasar ta mallaka ba.

Ribadu, wanda ya yi jawabi a wata liyafar godiya da aka shiryawa mambobin kwamitin da ya ke jagoranta a Abuja, ya bukaci tawagar yakin zaben da ta sake zage damtse wajen gudanar da ayyukanta a yayin da za a gudanar da zabukan gwamnoni da 'yan majalisun dokoki.

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, wanda ya ce za a saka masu kan wannan kokari na su, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bukaci zabukan gwamnoni da 'yan majalisun dokoki da zai ba shi damar gudanar da ayyukan ci gaba a kasar ba tare da tsaiko ba.

KARANTA WANNAN: Duba cikakken sunayen zababbun 'yan majalisar wakilan tarayya 24 na jihar Kano

Babu tantama: Yan Nigeria sun sake zabar shugaban kasa mai gaskiya - Ribadu
Babu tantama: Yan Nigeria sun sake zabar shugaban kasa mai gaskiya - Ribadu
Asali: Twitter

Ya ce: "Za mu ci gaba da kasancewa cikin farin ciki na tswon shekaru hudu saboda mun yiwa kasar wani gagarumin aiki, na sake zabar shugaba mai adalci. Buhari mutum ne na-gari. Yana cike da adalci a shugabancinsa. Zai kare kadarori da arzikin kasa. Ba zai taba barin bata-gari su zalunci jama'a da sace masu dukiyar kasa ba. Kuma wannan ne muke so mu gani a matsayin shugabanmu.

"Ba zai je ya sayar da Nigeria ba. Ba zai taba sayar da duk wasu kadarori da muka mallaka ba. Mu kuma ba zamu yi tarayya da duk wanda zai kawo mana matsala ko wani al-kaba'i ba. Ba zamu lamunci masu yunkurin satar dukiya jama'a ba," a cewar Ribadu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel