Hatta da shanunmu na cike da murnar dawowar Shugaba Buhari - Miyetti Allah

Hatta da shanunmu na cike da murnar dawowar Shugaba Buhari - Miyetti Allah

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, Alhaji Bello Bodejo, ya bayyana cewa hattana da shanunsu na murnar samun nasarar sake lashe zaben shugaban kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Bodejo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya gabatar da jaridar The Sun, inda ya kara da cewa, nasarar Buhari ta haifar da wata nutsuwa a fadin tarayyar Nijeriya.

A yanzu ne ma za'a ga hakikanin canji. Ina da tabbacin Baba zai kawo wa Nijeriya canji mai tarin yawa. Shanu ma da ke dawa na murnar wannan nasara da aka samu domin su ma canji zai kai garesu."

A ranar Larabar da ta gabata da na zo tatsar nono daga shanuna, sai na fahimci nonon da na samu ya ninka abinda na saba samu. Wannan ko shakka babu ya nuna cewa wani kyakkyawan al’amari zai zo wa Nijeriya, wannan kuma shi ne ya sanya shanunmu cikin nishadi."

Kafin wannan lokaci, a duk bayan zabe akan samu nau’e-nau’en tashin hankali, amma wannan da Buhari ne yayi nasara, ji ka ke shiru. Kowa na cikin murna da farin ciki; ana ta raye-raye a wasu wuraren wasu ma har dabbobi su ke yankawa don nuna godiyarsu ga Ubangiji."

"Mu Fulani muna yi masa addu’a kuma mana fata zai tuna da mu. Al’ummar Fulani na cikin wani hali a kasar nan. Ana kashemu a kulli yaumin, amma duk da haka muna tare da Buhari. Mun aminta da shi domin namu ne, danmu ne, ubanmu ne kuma kakanmu ne."

Ina mai jan hankalinsa da ya gaggauta cire duk wani wanda ke kewaye da shi wanda ke cin dunduniyarsa. A lokacin yakin neman zabe, ‘yan takara da ‘yan siyasa da damu ciki har da Atiku sun so su yi amfani da wata dama su rudemu da cewar Buhari bai tsinana mana komai ba."

"Amma mun fahimci cewa Buhari ya kama aiki ne a lokacin da kasar ke cikin halin Lahaula. Muna da cikakken yakinin cewa yanzu Buhari zai yi aikin ciyar da Nijeriya gaba sama da yadda ya yi a baya.

"Mun ki yarda a saye da kudi saboda zato da muka kyautatawa Buhari, kuma muna fata Buharin zai saurari shugabancin kungiyar Fulani.,” inji Bodejo.

Game da zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar mai zuwa kuwa, Bodejo yay i fatan rashin nasara ga dukkan gwamnonin da ke kokarin kafa dokar hana kiwo da samar da burtalai. Ya kara da cewa dukkan gwamnonin da ba sa son Fulani, ko shakka babu makiya Nijeriya ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel