Yanzu yanzu: Jirgin horas da daliban kwalejin NCAT ya yi hatsari a Kaduna

Yanzu yanzu: Jirgin horas da daliban kwalejin NCAT ya yi hatsari a Kaduna

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu, na nuni da cewa daya daga cikin jiragen yakin sama da ake amfani da shi wajen horas da daliban kwalejin koyon fasahar tukin jiragen sama ta kasa (NCAT), Zaria, jihar Kaduna, ya rikito ba shiri, inda ya yi hatsari.

A cewar majiya mai tushe, matukin jirgin horon, kirar TB-9, ya samu nasarar saukar da jirgin kasa, bayan da ya rikito da shi daga sararin subuhana, inda ya dira a kusan mil 7 daga Arewa maso Yammacin filin jiragen sama na Kaduna a ranar Juma'a.

KARANTA WANNAN: Siyasa: An dakatar da EFCC daga binciken jirgin da aka kama makare da kudade

Sai dai wadanda ke a cikin jirgin ba su samu raunuka ba, kuma tuni suka koma sansaninsu da ke cikin garin Zaria.

Yanzu yanzu: Jirgin horas da daliban kwalejin NCAT ya yi hatsari a Kaduna
Yanzu yanzu: Jirgin horas da daliban kwalejin NCAT ya yi hatsari a Kaduna
Asali: UGC

Tuni dai hukumar gudanarwar kwalejin, ta bin dokokin da aka tanadar, ta sanar da hukumar binciken hatsurran jiragen sama ta kasa (AIB) kan wannan hatsari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel