Siyasa: An dakatar da EFCC daga binciken jirgin da aka kama makare da kudade

Siyasa: An dakatar da EFCC daga binciken jirgin da aka kama makare da kudade

Rahotanni sun bayyana cewa an haramtawa hukumar EFCC binciken jirgin 'yan kasuwa da aka kama makare da kudade a ranar 15 ga watan Fabreru, 2019, ana gabar zaben shugaban kada da na 'yan majalisun tarayya.

Jaridar PUNCH a ranar Juma'a ta ruwaito cewa jirgin, wanda aka shirya zai je Ilorin, jihar Kwara, daga filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, jihar Legas, ya gaza tashi sama saboda nauyin da kudaden suka yi masa.

Majiya daga bangarori da dama sun bayyana cewa jami'an hukumar EFCC sun isa inda jirgin ya tsaya bayan da suka kai ruwa rana da wasu mutane. Sun bukaci sanin inda kudin suka fito, mamallakinsu da kuma inda za a kai su.

KARANTA WANNAN: Ba gudu ba ja da baya: Ni cikakken dan PDP ne, ba zan koma APC ba - Dino Melaye

Siyasa: An dakatar da EFCC daga binciken jirgin da aka kama makare da kudade
Siyasa: An dakatar da EFCC daga binciken jirgin da aka kama makare da kudade
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suke a cikin jirgin sun shaidawa jami'an EFCC cewa an shirya amfani da kudaden ne wajen gudanar da zabe a jihar Kwara, sai dai bisa rahotanni, jami'an hukumar sun ki amincewa da wannan bayani, inda suka turje akan lallai sai sun tafi da kudaden.

"Sai dai, jami'an sun samu kira daga fadar shugaban kasa inda aka umurce su da su bar wajen jirgin kuma su cire hannuwansu daga loamarin. Jim kadan bayan hakan, wasu sojoji suka mamaye wajen, inda aka kwashe kudaden zuwa wani jirgin da misalin karfe 10 na dare suka tashi," a cewar wata majiya.

A hannu daya, bincike ya bayyana cewaq EFCC ba zata gudanar da bincike kan wani zargi da aka yiwa jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ba, na safarar makudan kudade da suka kai Naira 2bn, a gabar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Duk da cewa Tinubu ya yarda da cewa ya yi safarar makudaden kudaden zuwa gidansa da ke Ikoyi, wanda kuma ya sabawa dokar safarar kudade, bincike ya bayyana cewa hukumar EFCC ba ta da wani shiri na bincikar lamarin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel