Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari

Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari

Kungiyar Dattawa Arewa Initiative (KDAI) ta mika sakon taya murnar ta ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa nasarar da ya samu wurin lashe babban zaben da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Kungiyar ta ce ruwan kuri'u da sassan Najeriya da dama suka zuba masa ya nuna cewa ya samu amincewar 'yan Najeriya kan cewa zai cika alkawuran da ya dauka.

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da shugaban kungiyar Janar Paul Tarfa da mataimakinsa Mr Sani Daura suka fitar a ranar Juma'a a babban birnin tarayya a Abuja.

DUBA WANNAN: Wani miji ya kashe matarsa saboda hana shi raya sunar aure

Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari
Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari
Asali: UGC

"Wannan itace zabe na farko a tarihin Najeriya inda sassan kasar dukka suka bawa shugaban kasa kuri'u masu yawa.

"Yadda shugaban kasar ya samu kuri'u daga sassa da dama ba tare da la'akari da addini ko kabila ba ya cika ka'idan kundin tsarin mulki ne neman kashi biyu na uku na kuri'u daga dukkan jihohin Najeriya da babban birnin tarayya, Abuja.

"Wannan ya nuna karara cewa al'ummar Najeriya sun sunyi imani cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai iya cika alkawurran da ya dauka musu na inganta tattalin arziki, yaki da rashawa, samar da tsaro da sauransu."

Kungiyar hadin kan Afirka da sauran kasashen duniya sunyi amana da jajircewar da Buhari ya keyi wurin daura Najeriya kan turbar cigaba ta fannin tattalin arziki da zaman lafiya da dabbaka demokradiya mai dorewa, hakan yasa yanzu kasashen duniya ke girmama Najeriya kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel