Assha: Mutane 32 sun mutu a wani sabon hari da 'yan ta'adda suka kai Zamfara

Assha: Mutane 32 sun mutu a wani sabon hari da 'yan ta'adda suka kai Zamfara

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu na nuni da cewa wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutane 32, wadanda mafi akasarinsu mambobin kwamitin sa kai ne na karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.

Rahoton sabon harin da 'yan ta'addan suka kai ya bayyana ne a ranar Juma'a, kwanaki 2 bayan da aka kashe mutane 13 a irin wannan harin a kauyen Kawaye da ke karamar hukumar Anka.

Mazauna garin sun bayyana cewa 'yan ta'addan dauke da muggan makamai sun kai hari a wani sansanin bincike na kwamitin sa kai da ke kusa da Kware, wani kauye da ke kilomita 18 a gabashin garin Shinkafi, inda suka harbe su nan take.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Yan takarar gwamnoni 20 a Zamfara sun hakura, sun marawa APC baya

Assha: Yan ta'adda sun kashe mutane 32 a wani sabon hari da suka kai Zamfara
Assha: Yan ta'adda sun kashe mutane 32 a wani sabon hari da suka kai Zamfara
Asali: Twitter

"Kasuwar garin Shinkafi na ci a kowacce ranar Alhamis, 'yan kwamitin sa kai sukan tsare hanyar da ke zuwa kasuwar domin tabbatar da tsaron 'yan kasuwa. Sai dai, wasu 'yan ta'adda masu yawa dauke da muggan makamai haye akan babura, suka kai wa 'yan kwamitin hari. Sun kashe akalla 32, wasu kuma har yanzu ana kan nemansu" wani mazaunin garin, Ali Sani ya labarta.

Sai dai duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda na jihar kan wannan sabon hari ya ci tura har zuwa lokacin kammala wannan labari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel