Da duminsa: Yan takarar gwamnoni 20 a Zamfara sun hakura, sun marawa APC baya

Da duminsa: Yan takarar gwamnoni 20 a Zamfara sun hakura, sun marawa APC baya

- Akalla 'yan takara 20 na kujerar gwamnan jihar Zamfara daga jam'iyyu daban daban suka hakura da takararsu a zaben ranar 9 ga watan Maris mai zuwa

- Hon Zayanu Salisu, ya ce sun yanke wannan shawarar ne ta hada hannu da APC domin bunkasa demokaradiyya a jihar

- A na shi jawabi, gwamna Abdul-Aziz Yari ya jinjina masu bisa hangen nesan su, tare da yi masu godiya akan goyon bayan da za su baiwa jam'iyyar

Akalla 'yan takara 20 na kujerar gwamnan jihar Zamfara daga jam'iyyu daban daban suka hakura da takararsu a zaben ranar 9 ga watan Maris mai zuwa, inda suka marawa jam'iyyar APC baya domin bata damar lashe zaben.

Da ya ke gabatar da jaddawalin jam'iyyun siyasar da za su janye takararsu, dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APP, Hon Zayanu Salisu, ya ce sun yanke wannan shawarar ne biyo bayan zaman da suka yi tare da cimma matsaya ta hada hannu da APC domin bunkasa demokaradiyya a jihar.

"Mun aminta cewa, ta hanyar la'akari da irin ci gaban da jihar ta samu karkashin gwamnati mai ci a yanzu, ba mu da wani zabi da ya wuce mu marawa jam'iyya mai mulki baya a zaben gwamnoni da ke gabatowa" a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Mata sun mamaye Abuja, sun bukaci Atiku ya amince da shan kaye

Da duminsa: Yan takarar gwamnoni 20 a Zamfara sun hakura, sun marawa APC baya
Da duminsa: Yan takarar gwamnoni 20 a Zamfara sun hakura, sun marawa APC baya
Asali: Facebook

Ya ce tun tuni shuwagabannin jam'iyyun sun umurci magoya bayansu da za su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kadawa jam'iyyar APC kuri'un a zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki mai zuwa.

A na shi jawabi, gwamna Abdul-Aziz Yari ya jinjina masu bisa hangen nesan su, tare da yi masu godiya akan goyon bayan da za su baiwa jam'iyyar, yana mai ba su tabbacin cewa ba zai ware su daga cikin harkokin gwamnatin jihar ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel