Fadan manya: Cacar baki ta shiga tsakanin Oshiomhole da Rochas Okorocha

Fadan manya: Cacar baki ta shiga tsakanin Oshiomhole da Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Rochas Okorocha ya maidawa shugaban jam'iyyar ta APC a mataki na kasa Kwamared Adams Oshiomhole zafafan kalamai biyo bayan dakatar da shi din da aka yi.

Rochas, wanda yanzu haka ya lashe kujerar Sanata a shiyyar mazabar sa a APC din zaben da ya gabata yayi fatali da korar da aka yi masa yana mai zargin shigaban jam'iyyar ta APC da yunkurin jefa rudani a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar dake yankin Ibo.

Fadan manya: Cacar baki ta shiga tsakanin Oshiomhole da Rochas Okorocha
Fadan manya: Cacar baki ta shiga tsakanin Oshiomhole da Rochas Okorocha
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara

Legit.ng Hausa ta samu cewa Zababben Sanatan mai jiran gado ya kuma yi zargin cewa Kwamared Oshiomhole yana wata manufa ta musamman ce dake da alaka da zaben da za'a gudanar shekarar 2023 shi yasa yake neman tozarta shi.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa sabbin bayanai na kara fitowa game da sakamakon tattaunawar gaggawa ta sirri da shugabannin jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) suka gudanar da yammacin yau da aka ce sun dakatar da wasu jiga jigan ta daga jam'iyyar.

Kamar dai yadda muka samu, bayan gwamnonin jihar Imo da Ogun, Ibikunle Amosun Rochas Okorocha, jam'iyyar ta kuma dakatar da ministan Shugaba Muhammadu Buhari na ma'aikatar kula da yankin Neja Delta, Fasto Usani Usani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel