Rikita-Rikita: Bayan gwamnoni 2, APC ta dakatar da ministan Buhari daga cikin ta

Rikita-Rikita: Bayan gwamnoni 2, APC ta dakatar da ministan Buhari daga cikin ta

Sabbin bayanai na kara fitowa game da sakamakon tattaunawar gaggawa ta sirri da shugabannin jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) suka gudanar da yammacin yau da aka ce sun dakatar da wasu jiga jigan ta daga jam'iyyar.

Kamar dai yadda muka samu, bayan gwamnonin jihar Imo da Ogun, Ibikunle Amosun Rochas Okorocha, jam'iyyar ta kuma dakatar da ministan Shugaba Muhammadu Buhari na ma'aikatar kula da yankin Neja Delta, Fasto Usani Usani.

Rikita-Rikita: Bayan gwamnoni 2, APC ta dakatar da ministan Buhari daga cikin ta
Rikita-Rikita: Bayan gwamnoni 2, APC ta dakatar da ministan Buhari daga cikin ta
Asali: UGC

KU KARANTA: An yi zina da ma'aikatan mu a zaben da ya gabata inji INEC

Haka zalika a yayin zaman na shugabannin jam'iyyar APC, sun kuma sanar da yanke hukuncin su na dakatar da babban Daraktan kafar labarai ta muryar Najeriya watau Voice of Nigeria (VON) mai suna Osita Okechukwu.

Wannan dai kamar yadda muka samu na zaman mataki na farko na ladaftarwa da jam'iyyar tace ta soma dauka akan mutanen da ta zarga da yi mata zagon kasa a lokacin zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayyar da suka gabata.

Haka ma dai mun samu cewa jam'iyyar ta kuma aike da takardar gargadi da kuma neman bahasi zuwa ga gwamnan Ondo Mista Akeredolu domin jin ta bakin sa yadda akayi shugaba Buhari ya fadi jihar a zaben da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel